
05/09/2025
Shugaban darikar Qadiriyya, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ya bayyana cewa ba sa goyon bayan duk wani abu da ya saɓawa koyarwar Musulunci a yayin gudanar da Maulidi.
Ya ce abubuwa irin su shaye-shaye da raye-raye ba su da wata alaƙa da Maulidi, domin yin hakan saɓa wa manufar taron ne.
Sheikh Qaribullah ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake jawabi a Mauludin Makarantar Hadisi da aka gudanar a gidan Qadiriyya da ke Kabara, Kano.
Ya jaddada cewa manufar Maulidi ita ce tunatar da musulmi game da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammadu (SAW), tare da karantar da mutane darussa masu amfani.
A cikin jawabin nasa, Shehin ya kuma yi kira ga shugabanni da ƙasashen duniya da su gaggauta kawo ƙarshen rikicin Gaza, domin kare rayukan fararen hula da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga gwamnonin Najeriya da shugaban ƙasa da su ji tsoron Allah kan zubar da jinin al’umma, su yi duk mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen garkuwa da mutane, sata, kwacen waya da kuma ayyukan dabanci. Ya tunatar da su cewa idan sun mutu Allah zai tambaye su kan abin da s**a aikata