16/11/2025
Kungiyar Dei-Dei Volunteers Forum ta zama fitila mai haskaka al’umma, domin tana gudanar da muhimman ayyuka da s**a shafi ci gaban yara, matasa da daukaka yankin Dei-Dei gaba ɗaya. Daya daga cikin manyan ayyukan da ake alfahari da su shi ne shirin ilmantar da dalibai, wanda ya riga ya zama wata hanya ta farfado da sha’awar karatu, gyaran makoma, da samar da dama ga marasa galihu.
A cikin wannan shiri, malamai masu jajircewa daga cikin mambobin kungiyar suna keɓe lokacinsu don koyar da darussa kamar Mathematics, English, Science, da sauran muhimman fannoni ga ɗalibai daga SS1 zuwa SS3. Akwai darussa na musamman da ake ba waɗanda ke shirye-shiryen rubuta jarabawar WAEC, NECO da JAMB – domin tabbatar da cewa kowa ya samu horo mai inganci, komai matsayinsa.
Ayyukan Dei-Dei Volunteers Forum bai tsaya kawai a koyarwa kaɗai ba, shirin yana Fatan farfado da burin matasa, rage yawan yawo a tituna, inganta tarbiyya, ilimi da zaman lafiya a Dei-Dei. Hakika, wannan aiki haske ne , ya kuma tabbatar da cewa al’umma na iya bunkasa idan mutane s**a haɗa kai domin ganin cigaba.
A yau, Dei-Dei Volunteers Forum muna fata ta zama abin koyi ga Sauran kungiyoyi wajan tabbatar ta re da nuna cewa ilimi shine jarin da babu wanda zai taba kwacewa daga mutum. Ayyukan su hujja ce cewa idan al’umma ta ba matasa dama, za su iya haskaka gari fiye da yadda ake zato.
Na Gode!
Abu Mashkhoor
Chairman Dei-Dei Volunteers Forum