28/08/2025
“DAN DAKON ME CIKE DA BURI”
Yana daga cikin al’amuran rayuwa, mutum ya fara daga ƙanana kafin ya kai ga manya. Wanda ake gani a kasuwa yana ɗaukar kaya a kafaɗa, yana zagaya t**i cikin gumi da wahala, ba wai babu mafarki a zuciyarsa ba ne. A’a, akwai babban buri da yake nufi.
Hakika, burin mutum ba ya cika cikin sauƙi. Dole ne ka jure gumi, ka jure nauyi, ka jure wulakanci da zargi. Amma duk wanda ya dage, Allah zai saka masa da nasara.
Ka kalli ɗan dako, mai ɗaukar kaya – mutane da yawa suna ganin shi ƙarami, amma a zuciyarsa ya san cewa wannan hanya ce ta neman halal, hanyar da za ta iya kai shi ga gina gida, ilimantar da ‘ya’ya, da kuma samun mutunci a cikin al’umma.
Ya ku matasa, kada ku raina ƙananan ayyuka, kada ku raina sana’ar da take cikin gumi. Abin da kuke yi da gaskiya da halal, shi ne zai gina makomar ku.
Darasi:
Nasara tana cikin haƙuri da dagewa.
Halal, ko da ƙanƙane ne, ya fi haram mai yawa.
Wanda ya dage a kan sana’arsa da buri, Allah zai ɗaga darajarsa.
---Muh D Yusuf 625---✍️