17/09/2024
ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE
ℹ️ Lokacin da ake yin zikirin safiya shine daga bayan sallar asuba zuwa kafin rana ta ɓullo.
Lokacin da ake yin zikirin maraice kuma shine daga bayan sallar la'asar zuwa kafin rana ta faɗi.
Babu laifi musulmi ya yi su a bayan waɗancan lokutan da aka faɗa (ma'ana bayan lokacin da ake yin zikirin ya wuce), idan ya manta ko kuma wani uzuri ya bijiro mai sai bai samu damar yin su ba.
📘"فقه الأدعية والأذكار" للشيخ عبد الرزاق البدر.
"Fiqh Al'adeiat Wal'adhkar" Na Shaikh Abdulrazaƙ Albadri.
(1)
Karanta Ayatul-kursiyu. (sau ɗaya):
﴿اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ مَنْ ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِنْدَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ﴾.
Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye, Mai tsayuwa da komai. Gyangyaɗi ba ya k**a Shi, wala barci. Abin da ya ke cikin sammai da abin da yake cikin kasa nasa ne. Babu mai yin ceto a wurinsa sai da izininsa. Yana sane da abin da yake gabansu (wato al’amarin duniya) da abin da yake bayansu (na al’amarin lahira). Ba sa sanin wani abu daga iliminsa, sai abin da Ya so. Kursiyyunsa (wato gadonsa) ya yalwaci sammai da ƙasa, kuma kiyaye su (sammai da ƙassai) ba ya yi masa nauyi. Shi ne kuma Maɗaukaki, Mai girma.
Da kuma karanta waɗannan surori kowace (sau uku):
﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ...﴾،
﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ...﴾،
﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ...﴾.
(2)
(أَصْبَحْنَا وَأَصْبَحَ الْمُلْكُ لِلّٰهِ)¹، وَالْحَمْدُ لِلّٰهِ، لَا إِلَهَ إلَّا اللّٰهُ، وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ، وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، (رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ، وَخَيرَ مَا بَعْدَهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذَا الْيَوْمِ، وَشَرِّ مَا بَعْدَهُ)²، رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنَ الْكَسَلِ، وَسُوءِ الْكِبَرِ، رَبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنْ عَذَابٍ فِي النَّارِ وَعَذَابٍ فِي الْقَبْرِ.
Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, mulki ya tabbata gare Shi, kuma yabo ya tabbata gare Shi, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. Ya Ubangijina! Ina roƙonka alherin da ke cikin wannan rana, da alherin da ke bayanta. Kuma ina neman tsarinka daga sharrin da ke cikin wannan rana, da sharrin da ke bayanta. Ya Ubangijina) Ina neman tsari da Kai daga lalaci, da mummunan tsufa. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga azaba a cikin wuta, da kuma azaba a cikin ƙabari.
Idan da maraice ne sai ya ce:
¹(أَمْسَيْنَا وَأَمْسَى الْمُلْكُ لِلّٰهِ).
²(رَبِّ أَسْأَلُكَ خَيْرَ مَا فِي هَذِهِ الْلَيْلَةِ، وَخَيْرَ ما بَعْدَهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا فِي هَذِهِ الْلَيْلَةِ، وَشَرِّ مَا بَعْدَهَا).
¹ Mun shiga maraice, kuma mulki ma ya shiga maraice yana mai tabbata ga Allah.
² Ya Ubangijina! Ina roƙonka alherin da ke cikin wannan dare da alherin da ke bayansa. Kuma ina neman tsarinka daga sharrin da ke cikin wannan dare da sharrin da ke bayansa.
(3)
اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَا إِلَهَ إلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي، فَاغْفِرْ لِي، فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ.
Ya Allah! Kai ne Ubangijina; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, kuma ni bawanka ne; kuma ina kan alƙawarin da na yi maka (na kaɗaitaka da bauta) da kuma alƙawarin da Ka yi mini (na shigar da wanda bai yi shirka da Kai ba gidan aljanna) gwargwadon ikona. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina tabbatar da ni'imarka gare ni, kuma ina tabbatar da zunubi na; Ka gafarta mini, domin ba wanda yake gafarta zunubai sai Kai.
(4)
(اللَّهُمَّ بِكَ أَصْبَحْنَا، وَبِكَ أَمْسَيْنَا، وَبِكَ نَحْيَا، وَبِكَ نَمُوتُ، وَإِلَيْكَ النُّشُورُ)¹.