06/07/2025
MASU DUBA AYYUKAN NUKILIYA NA MAJALISAR DINKIN DUNIYA SUN FICE DAGA KASAR IRAN....
Masu duba mak**an nukiliya na hukumar IAEA ta Majalisar Dinkin Duniya sun bar Iran ranar Juma'a bayan kasar ta dakatar da hadin kai da hukumar, sak**akon rikicin kwanaki 12 da ya faru tsakanin Iran da Isra’ila, wanda ya haifar da harin jiragen sama na Isra’ila da Amurka a wuraren mak**an nukiliyar Iran. Wannan ya janyo tashin hankali tsakanin Tehran da hukumar IAEA...
Hukumar ta bayyana cewa tawagar ta fice daga Iran lafiya, suna komawa hedkwatar hukumar a Vienna, bayan sun kasance a Tehran a lokacin rikicin soja. Daraktan IAEA, Rafael Grossi, ya jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa da Iran domin sake farfado da ayyukan sa ido da tabbatarwa cikin gaggawa...
Iran ta dakatar da hadin kai da IAEA a hukumance ranar Laraba, bayan majalisar kasar ta amince da dokar da ke tabbatar da kare hakkin kasar a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar mak**an nukiliya, musamman ma game da bunkasa sinadarin uranium....
Amurka ta soki wannan mataki na Iran, tana mai cewa ba abin karɓa bane, tare da kira ga Tehran da ta dawo kan teburin tattaunawa da aka katse sak**akon harin soja na Isra’ila a watan Yuni...
A gefe guda, Isra’ila ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan da s**a dace don tunkarar Iran, har da dawo da takunkumi kan kasar, yayin da ta yaba da nasarorin da sojojinta s**a samu a yakin kwanaki 12 da s**a gabata, duk da dai a zahiri ita Isra’ila ce tafi ɗanɗana kuɗarta...
A takaice, wannan lamari ya kara tsananta rikicin siyasa da na tsaro a yankin, tare da jefa al’amuran nukiliyar Iran cikin yanayi mai cike da rashin tabbas...
To Madallah....