11/09/2026
DA DUMI-DUMI: Mabiyan Shiekh Musa Lukwa sun kashe mutumin da ya yanke shi da wuka a Sokoto
An kashe wani matashi da ake zargi da daba wa wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukwa, wuka jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a masallacinsa da ke yankin Mabera, cikin birnin Sakkwato.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda rahotanni s**a ce matashin, wanda ake kira Mai Barewa, ya kasance cikin masu ibada a masallacin, kafin ya farmaki malamin tare da daba masa wuka sau biyu a wuya bayan kammala sallar.
Majiyoyi sun ce masu ibadar da ke wurin sun yi nasarar cafke wanda ake zargin, inda daga bisani s**a yi masa duka har ya mutu.
Rahotanni sun danganta harin da wata huduba da Lukwa ya gabatar a baya, inda ya ambaci wani Hadisi da wasu malaman addini, musamman masu alaƙa da ɗariƙar Sufaye s**a ce ya ɓata sunan iyayen Annabi Muhammad (SAW).
Bayan wannan cece-ku-ce, an ce Mai Barewa ya yi barazanar kashe Malam Lukwa da babban ɗalibinsa, Malam Murtala Assada.
Malamin da mabiyansa sun kai rahoton barazanar ga ’yan sanda, lamarin da ya kai ga k**a matashin da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. Kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na wani lokaci, yayin da shari’ar ke ci gaba.
Kwanaki huɗu kafin harin na Juma’a, Malaman sun kuma ziyarci fadar gwamnatin jihar Sakkwato, inda s**a gabatar da rubutacciyar ƙorafi kan lamarin.
Da yake tabbatar da faruwar harin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce Malam Lukwa na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Sakkwato.
Ya ce mabiyan malamin ne s**a kashe wanda ake zargin bayan sun cafke shi.
Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa kawo yanzu ba a k**a wani mutum dangane da tashin hankalin ba, sai dai rundunar ta ɗauki matakan da s**a dace domin hana lamarin ƙara ta’azzara.
Ya ce ’yan sanda na gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa harin da kuma gano duk mutanen da ka iya kasancewa da hannu a lamarin.