30/08/2025
Ta yaya 'yan kudu zasu daina mana kallon wawaye har su daina ƙiranmu da 'ABOKI'?
A iya shekaru 2 na mulkin Tinubu, jihar Lagos kaɗai ta samu ayyukan da s**a haura naira tiriliyon 3 da biliyon ɗari tari (₦3.9trn) a yayin da arewa da s**a haɗa da Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Niger, Gombe, Adamawa, Borno, Yobe, Bauchi, Taraba da kuma jihohin yankin Inyamurai, gaba ɗayansu, s**a samu naira tiriliyon 3 da biliyon ɗari biyar (₦3.5trn)
Ba wannan ne abin takaicin ba, domin dama ya samu ya ke amfani da damarsa don gina yankinsa, abin takaicin shi ne, da zarar talakawa sun fara ƙiran cewar lallai a tina masa cewar a yankin arewa fa ya samu ƙuri'u, ya zo ya magance matsalolin yankin musamman na tsaro, sai ka ji wawayen cikinmu suna cewa su dai MUZLUM-MUZLUM! Kuma suna faɗa da alfahari, kuma wasun ma suna da mabiya, wawayen mabiyan kuma sai su biye su suna ganin kamar hakan wata gwaninta ce ko abin burgewa, ko kuma iya abin da mu ke buƙata kenan a arewa.
Kenan dai matuƙar Tinubu da Kashim suna nan a matsayin Musulmai, to mu iya Musuluncinsu ya biya mu, ba mu da wata buƙata daga garesu.
To muna addu'ar Allah Ya dawwamar da su a cikin Musulunci har mutuwarsu.
Do Allah gaya min dalilin guda ɗaya da zai hana ƴan kudu su daina mana kallon wawaye har su daina ƙiranmu da 'ABOKI'?
✍️ Muhammed Auwal Ahmed