24/08/2023
Alaƙar sabon kwamishinan matasa da wasanni na Yobe da Matasa tun shekarar 1999.
.....Hon. Barma Shettima.
A shekarar 2019, a dai-dai lokacin da ƴan majalisan dokokin Jahar Yobe suke tantance sabbin kwamishinoni (ciki har da Hon. Barma Shettima), sai Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Machina Alh. Kachalla Ajiya Machina ya tashi yace "A tarihin karamar hukumar Machina bamu taɓa samun shugaban karamar hukuma wanda ya dauki matasa da yawa aiki k**ar HON. BARMA SHETTIMA ba, haka zalika bamu taba samun shugaban karamar hukuma wanda ya jawo matasa jiki k**ar shi ba. Kasancewarsa shugaban karamar hukumar Machina a shekarar 1999, muna jinjina masa sosai".
Daga baya sai nayi wani karamin bincike, sai na tabbatar da cewa Hon. Barma masoyin matasa ne na hakika.
(a) Idan kaje gidansa, babu wadanda zaka gani sai matasa.
(b) idan kaje office nasa, babu wadanda zaka gani sai matasa,
(c) duk lokacin da ka kai masa matsalar da ta shafi matasa zai saurare ka, kuma zai tsaya don kawo masalaha,
(d) Bayo son yaga an danne hakkin matasa.
Kafin shekrar 1999, duk karamar hukumar Machina Masallatan Juma'a guda biyu ne kachal, amma daga 1999-2003 ya gina Masallatan Juma'a guda 18 , ya sauka akan mulki Machina tana da Masallatan Juma'a guda 20 ( source Auwalu Isa Dankwanyo )
Haka zalika, a zamaninsa bayan ayyukan cigaba da ya kawo, ya kafa tarihi wajen ayyukan cigaban matasa, inganta rayuwar matasa da jawo matasa jiki.