30/07/2025
Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!
Ziyara domin ciyar da Nguru Gaba Dama Jihar Yobe Baki daya, wacce Sabon Shugaban Makarantar Ilimi ta Nguru (Atiku Abubakar Colleage Of Legal and Islamic Studies Nguru) Prof Ali Usman Manzo' Kenan a Yayin da yakaiwa Hon. Abubakar Abubakar jinjiri (AAJ) ziyarar a ofishinsa Dake Abuja.
Wannan ziyarar ziyarace ta Musamman da Shugaban Makarantar yakaiwa Alhaji. Abubakar Abubakar jinjiri (AAJ) wacce ke kunshe da Taun manufofi na Alheri, Kuma ta kunshi manufofi masu Tarin gaske domin ciyar da Nguru da Al'ummar Nguru Gaba.
Prof, Ali Usman Manzo' Yayi tattakinne domin samun Co-operation tsakaninsu manya Kuma haifaffun garin Nguru, masu son Cigaban Nguru,domin Yana da manufa dayawa akan chanja salon makarantar Dama kawo wasu kwasa-kwasai wayenda ba'ayida, Dama wasu abubuwa masu mahimmanci Wanda bazasu fadu anan ba bissa wasu dalilai.
Hon. AAJ' ya karbeshi hannu Biyu Biyu, ya Kuma nuna Farin cikinsa ga Prof, bisa wannan nazari Babba da Yayi akan ziyartar manyanmu, hakika AAJ yaji dadi Sosai da Sosai, Kuma ya yabawa Prof, ya kara tabbatarmasa cewa ana tare dukkan sanda akaga abinda zaikawo cigaba Yana maraba dashi, kofarsa a bude take ko yaushe.
Hon.AAJ, ya sake tabbatarwa da Prof, Manzo' cewa bashi da wani buri daya Wuce yaga nguru da Al'ummar nguru sunci Gaba, Yakara dacewa bawai kawai siyasa bace kadai alakarsa da mutanan Nguru ba, akwai kauna Mai karfi a tsakani Wanda Allah ne kawai Yasan irin wannan kaunar Dake tsakaninsa da mutanan Nguru Baki daya.
Prof. Manzo' yaji dadi matuka ya kuma yabawa AAJ bisa irin niyyarsa akan Garinmu, da Kuma irin yanda yakeso yaga ankawo abinda zaikawo Chanji da Garinmu da mutananmu Baki daya' Prof, Yamasa Godiya Sosai.
Kowa Yasan waye Prof, Ali Manzo' akan bugatarsa bazaije wajenkaba nasanshi, nasan wanene shi.
Allah Yasake kawo Cigaba Mai amfani, shi Kuma Allah Yasa yafara lafiya ya gama lafiya, Allah Yabiyamasa dukkan wani burinsa akanmu Amin.
Hon.AAJ MEDIA CREW.