Yobe social media

Yobe social media Wannan shafin Zai dinga kawo muku Abinda yake faruwa daga nan jahar Yobe da kuma tarayyar Nijeriya Gaba ɗaya

Ya zama dole iyaye su rinka hakuri da binciken waye zasu bawa auren yayansu. Jiya misalin karfe 02:19 na dare na shawo k...
06/05/2025

Ya zama dole iyaye su rinka hakuri da binciken waye zasu bawa auren yayansu.

Jiya misalin karfe 02:19 na dare na shawo kwana dai dai court road kawai naga wannan baiwar allah da goyo kuma ga mijinta abaya da bulala yana korata wai sai ta tafi gidan iyayen ta a wannan mummunan daren, duk sabida wai yasata ta dafa masa abinci karfe 1:30 na dare ta dora bacci ya dauketa ta mance.

Tabbas wasu mazan idan s**ai wani aikin dabba ma bazataiba wallahi muna Allah wadai da irin wayannan mazan.

Kuma so da dama wallahi iyaye ke jefa yaransu a hannun irin wayannan jakn mazan allah y kyauta.

Daga Aminu Tura Hadejia

HARIN TA'ADDANCI A BAUCHIWasu 'yan ta'adda a jihar Bauchi sun kai harin ta'addanci a garin Duguri dake karamar hukumar A...
06/05/2025

HARIN TA'ADDANCI A BAUCHI

Wasu 'yan ta'adda a jihar Bauchi sun kai harin ta'addanci a garin Duguri dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi inda s**a hallaka mutane 19

Cikin wadanda s**a hallaka akwai 'yan banga wanda s**a fita fagen daga s**a sadaukar da rayuwarsu domin wasu su rayu ta hanyar yin arangama da 'yan ta'addan

Wannan yana daga cikin manyan hari na ta'addanci mai muni da ya faru a Bauchi bayan shafe wasu shekaru masu yawa

Alkaleri yana yankin da aka fara tono Rijiyar man fetur na farko a yankin Arewacin Nigeria, idan sun kai ta'addanci gurin kar ayi mamaki

Sai dai ta'addanci ba zai taba samun gurbin zama ba a Bauchi Insha Allah, zamu bada shawara zuwa ga Maigirma Gwamna, sauran bayanan sun shafi sirri

Muna rokon Allah Ya karbi shahadar wadanda s**a rasa rayukansu a wannan mummunan hari na ta'addanci
✍️ Datti assalapy

ATIKU FA LOKACI YAYI INSHA ALLAH Muna kyautata tsammani a yau Talata jagoran siyasarmu a Nigeria Alhaji Atiku Abubakar m...
06/05/2025

ATIKU FA LOKACI YAYI INSHA ALLAH

Muna kyautata tsammani a yau Talata jagoran siyasarmu a Nigeria Alhaji Atiku Abubakar mai tausayin talakawa zai bayyana matsayarsa game da siyasar 2027 mai karatowa

Muna kyautata zato Atiku da Peter Obi sun fahimci juna, sun amince suyi hadaka domin a ceto Kasar nan daga hannun mutanen da basa tausayin talakawan Nigeria sam

A yanzu Jam'iyyar PDP ta dauko hanyar mutuwa domin shugabanninta Tinubu suke yiwa aiki, duk wani Gwamna ko wani babban dan siyasa da ya bar PDP ya koma APC ya koma ne don neman mafaka akan barnan da yayi ba wai don kishin talakawa ba

A zaben 2023 da ya gabata mafi yawan Gwamnonin PDP ba suyi Atiku ba, mun san Gwamnonin da kwantawa s**ayi lokacin zaben Shugaban Kasa, amma duk da haka ratar dake tsakanin Atiku da Tinubu ba mai yawa bace

Peter Obi ba shi da Gwamna, bashi da Sanata, bashi da dan Majalisar tarayya har mafi karamin mukami wato kansila ko daya bashi da shi a zaben 2023, amma sai da ya samu kuri'u sama da Miliyan 6, yaci jihohi 11 har da birnin tarayya Abuja

A yanzu yadda s**a shirya tsarin cin amanar PDP da kokarin wargaza PDP din, haka mutanen da suke komawa jikinsu zasu ci amanarsa su taimaka wajen kayar da su

Duk abinda Tinubu zai yi walau murdiyan zabe ko amfani da kudi da karfin iko, to da ikon Allah sai Baba Atiku jagoran talakawa da Peter Obi sun kayar da shi a zaben 2027 Insha Allah

Daga Datti Asslafiya

AREWA FA MUN ZAMA BUZUHotunan barnan da 'yan ta'addan B0k0 Har@m s**ayi kena a jihar Yobe, sansanin Sojoji guda s**a kwa...
05/05/2025

AREWA FA MUN ZAMA BUZU

Hotunan barnan da 'yan ta'addan B0k0 Har@m s**ayi kena a jihar Yobe, sansanin Sojoji guda s**a kwace, s**a halaka Sojoji ki$sa na wulakanci

Maimakon mutanen Arewa da muke media hankalin mu ya koma kan batun dawowar ta'addancin B0k0 Har@m don a dauki mataki saboda matsalace da zata shafi kowa, amma sam wannan bai dame mu ba

Sai muka mayar da hankali akan batun shirme, ana ta musu akan cewa tsakanin mawaki Rarara da marigayi Mawaki Mamman Shata wa yafi wani iya waka?

Imban rashin sanin ciwon kai da wauta irin na mutanen Arewa ga matsala mai girma da ya k**ata ku mayar da hankali a kai kun barta kunzo kuna ta musu akan mawaka

Wannan yana kara nuna mana cewa Arewa ta kare, buzun Arewa ne kawai ya rage, an riga da an cinyemu da yaki, 'ya'yan mu da jikokin mu ba zasu taba yafe mana cin amanarsu da mukayi ba

Allah wadaran naka ya lalace

BOOOOM BUNI AIKI KOMAI DARE💥💥💥Da Misalin Ƙarfe 12:30 Na Dare Na Fito Zani Teaching Hospital, Kwatsam Saina Tarar Da Shug...
05/05/2025

BOOOOM BUNI AIKI KOMAI DARE💥💥💥

Da Misalin Ƙarfe 12:30 Na Dare Na Fito Zani Teaching Hospital, Kwatsam Saina Tarar Da Shugaban Hukumar Gyaran Hanyoyi Ta Jahar Yobe (YORMA) Wato Engr. Tijjani Hamisu Tare Da Hazikan Ma'aikatan Sa Suna Aikin Gyaran Titin Bakin Cross Na Tsakiyar Garin Damaturu Gabanin Fara Ruwan Sama, Insha Allahu Daga Yanzu An Daina Samun Tsaiko Da Taruwar Ruwa Bakin Cross Lokacin Damina.

Allah Ubangiji Ya Tabbatar Da Alheri.
✍️ Ahmad lamara

ALLAHU AKBAR: Yau Shekaru 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua.Tsohon shugaban ka...
05/05/2025

ALLAHU AKBAR: Yau Shekaru 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua.

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Marigayi Umaru Musa 'Yar Adua ya cika shekaru 15 da rasuwa, an yi jana'izar 'yar Adua a ranar 5 ga watan May 2010 a mahaifarsa da ke Katsina.

Ya samu kyakkyawar shaida daga mutane musamman ayyukan da ya yi a lokacin mulkinsa. Dame zaku iya tuna 'Yar Adua?

Gobe Hutu Ne A Katsina, Domin Samun Damar Fitowa Tarbar Shugaba Tinubu Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa Ya A...
01/05/2025

Gobe Hutu Ne A Katsina, Domin Samun Damar Fitowa Tarbar Shugaba Tinubu

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa Ya Ayyana Gobe Juma'a A Matsayin Ranar Hutu Ga Daukacin Ma'aikatan Jihar Katsina, Domin Ba Su Damar Tarbar shugaban Kasa Bola Tinubu, Wanda Zai Kawo Ziyarar Aiki Domin Ƙaddamar Da Wasu Ayyukan Gwamna Dikko Radda Da Kuma Halartar Ɗaurin Auren Diyarsa A Ranar Asabar.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

NEGF: The governors of the six states arrived at the venue for the opening ceremony of their 11th meeting held in Yobe S...
01/05/2025

NEGF: The governors of the six states arrived at the venue for the opening ceremony of their 11th meeting held in Yobe State.

The meeting provides a platform for the governors to discuss pressing issues, share experiences, and collaborate on initiatives that promote the development and well-being of their states.

The NEGF is essential for promoting the economic, social, and cultural development of the Northeastern region.

More details follow.

Ibrahim Baba Saleh
SSA Media and Public Engagement

Gobara ce ta k**a a Giwa Barrack na Maiduguri kuma ya taba manyan mak**ai na sojoji shiyasa manyan mak**ai suke ta fashe...
01/05/2025

Gobara ce ta k**a a Giwa Barrack na Maiduguri kuma ya taba manyan mak**ai na sojoji shiyasa manyan mak**ai suke ta fashewa, har hankalin mutane ya tashi.

Ana shawartar mutanen da ke kusa da wurin da su zauna a cikin daki don gudun kada wani makami ya fado kan al-umma.

DA DUMI DUMI: 2027 Munyi kyakkyawan Tsari Hatta Wanda Ba'a Haifaba Zamuyi Masa Albashi idan kuka Sake Bamu dama a karo n...
01/05/2025

DA DUMI DUMI: 2027 Munyi kyakkyawan Tsari Hatta Wanda Ba'a Haifaba Zamuyi Masa Albashi idan kuka Sake Bamu dama a karo na biyu, Bola Tinubu ga yan Nigeria

Me Zaku Ce

Ba zamu iya Gyara muku ko Bakü kariya dağa Ambaliyar Ruwa ba, Sakon Gwamna ga Yan Jahar Yobe
01/05/2025

Ba zamu iya Gyara muku ko Bakü kariya dağa Ambaliyar Ruwa ba, Sakon Gwamna ga Yan Jahar Yobe

Address

Damaturu

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Yobe social media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Yobe social media:

Share