Wagsoon Mallam

Wagsoon Mallam Allah first
Islam is the best�

04/07/2025

Almighty. We pray for strength and courage in these difficult times. There’s a lot of anxiety and uncertainty gripping many of us. You know what’s going to happen and You’ve promised to bring good out of every situation. We lay our trust in You; our greatest source of Hope. Aameen.

04/06/2025

🟤Muna neman tsarin Allah daga ta6ewa "su mutane idan s**a rasa abinda za su aibata wani da shi, kuma hassada tayi galaba akansu sabida adawa, sai kaga sun qirqiro masa abun aibu.🟤

Ibnul Araby.

03/06/2025

◾YA AKE RABA NAMAN LAYYA?◾

🟥1- Ana ci.

🟪2- Ana yin kyauta.

🟧3- Ana yi. Sadaka.

🟥Manufar yin layya guda uku ce :

♦️1- Jin dadin naman ta hanyar ci.
♦️2- Neman lada a wajan Allah ta hanyar yin sadaka.
♦️3- Nuna qauna ga mutane ta hanyar yimusu kyauta.

Uthaimin

30/05/2025

♦️AZUMTAR RANAR ARFA♦️

🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Azumin ranar arfa, ina sa rai daga Allah cewa zai kankare zunubin shekarar da ta gabata, da wadda za tazo a bayanta.🌹🌹

Muslim

26/05/2025

Ga fa'idodin kwanaki goma na Zul-Hijja (10 na farkon watan Zul-Hijja) a cikin Hausa:

Fa'idodin Kwanaki Goma na Zul-Hijja:

Su ne mafi alherin kwanaki a shekara: Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Babu wani lokaci da ayyukan alheri suke fi so da karbuwa a wurin Allah kamar wadannan kwanaki goma.”
(Hadisi daga Bukhari)

Ana samun lada mai yawa: Yin ibada kamar sallah, azumi, sadaka da zikiri a cikin wadannan kwanaki yana da lada mai girma.

Yin azumi na rana tara (Arafah): Azumin ranar Arafah (rana ta 9) yana kaffarar zunuban shekara biyu — na baya da na gaba.

Ranar Layya (Eid-ul-Adha): Rana ta 10 ita ce ranar babbar sallah, kuma yin layya yana daga cikin ibada mafi girma.

Zikiri da ambaton Allah: Akwai umarni na yin takbiri, tahmidi da tahlili (Allahu Akbar, Alhamdulillah, Laa ilaha illallah) a cikin wadannan kwanaki.

Yin Hajji: Wadannan kwanaki suna daga cikin lokacin da ake gudanar da aikin hajji, daya daga cikin rukunnan Musulunci.

Ranar Arafah tana da girma: Ita ce rana mafi girma cikin kwanaki, kuma addu’ar ranar Arafah tana karbuwa.

Suna cike da albarka: Allah ya rantse da wadannan kwanaki a cikin Al-Qur’ani:
“Ina rantsuwa da alfijir, da daren goma (na Zul-Hijja).” (Surat Al-Fajr: 1-2)

Damar neman gafara da tuba: Su ne lokaci mai kyau na tuba da neman gafarar zunubi.

Karfafa dangantaka da Allah: Yin ayyukan ibada a wadannan kwanaki yana kara kusanci da Allah.

26/05/2025

☘️Ya Ubangiji Ka Qaramana Kada Ka Ragemana, Ka Karrama Mu Kada Ka Wulaqantamu, Ka Bamu Kada Ka Hanamu.🤲

🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Haqiqa Allah S.W.T ya yimin wahayi akan cewa ku yi qanqan da kai, tayadda babu wanda zai ringa yiwa wani alfahari, kuma kada wani ya ringa zalintar wani.🌹🌹

Muslim

23/05/2025

🌹🌹An kar6o daga Abu hurairah R.A, haqiqa Ma'aiki S.A.W ya ga wani mutum bai wanke dugadugansaba a alwala sai yace : Tsananin narko na wuta, ya tabbata ga dugadugai wadanda ba'a wankewa.🌹🌹

Muslim

26/04/2025

☘️Ya Ubangiji Ka Shiryeni Izuwa Ga Gaskiya Cikin Abinda Akayi Sa6ani Akansa Da Izininka, Domin Kai Ne Mai Shiryarda Wanda Kake So Izuwa Tafarki Madaidaici.🤲🏼

🌹🌹An kar6o daga Abu Hurairah R.A yace : Manzon Allah S.A.W yace : Haqiqa Allah S.W.T zai ce a ranar alqiyama, ina masu soyayya sabida girmana ? A yaune zan sanyasu a qarqashin inuwata, ranarda babu wata inuwa sai inuwata.🌹🌹

Muslim

21/04/2025

🔳Mafi haduwar mutum shi ne wanda ba zai canja makaba ko da kuwa me ya faru a rayuwa.🔳

Najib Mahfuz.

20/04/2025

☘️Ya Ubangiji Ka Tabbatarda Ni Akan Tabbataccen Zance A Duniya Da Lahira.🤲🏼

🌹🌹An kar6o daga Abdillahi bn Amr R.A yace : Haqiqa Annabi S.A.W yace : Idan alqali yayi hukunci, yayi ijtihadi kuma yayi daidai, yana da lada biyu, idan kuma alqali yayi hukunci, yayi ijtihadi, sannan yayi kuskure, yana da lada daya.🌹🌹

Bukhari

Address

Nasarawa Bututu Street
Damaturu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Wagsoon Mallam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share