04/03/2026
Gwamna Bala Ya Yi Afuwa Ga Fursunoni 73 a Bauchi, Ya Biya Tara Ta Naira Miliyan 3.8
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya yi afuwa ga fursunoni 73 da ke zaman gidan gyaran hali a fadin jihar, inda ya yi amfani da huruminsa na kundin tsarin mulki karkashin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).
Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin wani biki da aka shirya domin sakin fursunonin, inda ya bayyana cewa yin amfani da ikon afuwa wani nauyi ne da kundin tsarin mulki ya dora masa, wanda ya ginu kan jin kai, adalci da tausayi—musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan.
Ya ce matakin ya biyo bayan nazari mai zurfi da kuma shawarwarin da Majalisar Ba da Shawara kan Ikon Afuwa ta jihar ta gabatar.
Bugu da kari, gwamnan ya amince da bayar da naira dubu dari (₦100,000) ga kowanne daga cikin wadanda aka yi wa afuwar domin tallafa musu wajen sake shiga cikin al’umma da kuma fara sabuwar rayuwa.
A nasa bangaren, Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Hassan Elyakub, ya bayyana cewa gwamnan ya kuma fitar da naira miliyan 3.8 domin biyan tara da diyya ga wasu daga cikin fursunonin da hukuncinsu ya hada da biyan kudade.
Ya kuma yi kira ga bangaren shari’a da su rika la’akari da amfani da hanyoyin hukunci na daban da ba na zaman gidan yari ba, kamar aikin al’umma, musamman ga masu kananan laifuffuka.
Shi ma Kontrolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya a Jihar Bauchi, Tade Monday, tare da wasu shugabannin addini, sun yaba da wannan mataki na jin kai da gwamnan ya dauka, tare da yin kira ga wadanda aka sako da su kasance masu bin doka da oda, tare da bayar da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban al’umma.