26/05/2025
DAGA BAKIN MAI ITA
AYI GYARA DON SAMUN NASARA A ZABEN 2027
Asslm.
Kamar yadda nayi alkawari , To Allah cikin rahamarsa ya tashemu lfy.Masha Allah.bayan tsokaci da nayi kan rashin Jagora daya tilo a Jam,iyarmu (APC) a jiharmu ta Bauchi, Kowana gidan siyasa na bin Jagoransu ne kawai a matakin tafiyarsa. Misali:-Senator Shehu Umaru Buba shine jagoran APC a Jiha, saboda Jama'ar sa sunna cewa shine kadai zababbe kuma tilo a Jiha, a cewar su sauran duk nadaddu ne.
Sai gidan Amb.Yusuf Mai Tama Tugga, haka take a wajen jama,arsa shine Jagora a APC ta jihar Bauchi, dalilin su shine cikakken dan siyasa wadda kuma ya jima yana gwagwarmaya a siyasance kuma haka ya ganta (Siyasa) a gidansu don haka dan na gada yafi dan na koya.
To haka gidan Dr.Ali Pate, Shima a wajen mutanen sa shine Jagoran APC a jihar don ya jima yana gwagwarmaya sannan a siyasance kuma Shima kamar Amb Yusuf Mai Tama Tugga , yayi takara gomna a lokaci dabam-dabam a Jam,iyu dabam dabam.
Abun da kuma ya dauki hankalin mutane shine a APC summit da akayi a Abuja sai ga H.E. Dr Isa Yaguda ya Jagoranci APCn jihar Bauchi a wajen taron duk da kasancewar ministoci biyu a wajen taron, sannan ga tsohon Gomnan Jahar Bauchi H.E. Muhammad A. Abubakar SAN, tsohon Dan takarar Gomna na jam'iyar Air Marshal Sadique Baba Abubakar da Malam Ya,u Darazo (National political Adviser) duk a wajen.
A gaskiya tunda shugaban kasa ne da Kansa ke nada jagora a Jiha, to ya Kamata shugaban jam'iyar APC na kasa H.E Abdullahi Umar Ganduje ya samu shugaban kasa akan samar da Jagora a jihar mu. Idan akayi nawa ko jinkiri to abin ba Zai haifar da nasara ko zaman lfy ma jam,iyar ba, domin kowa yana da mutanen sa kuma shi kadai suke sauraro.
Matsalar jam'iyar a sama shine bata sakawa mutanen da s**a mata wahala da alheri, mutane sai bayan sunyi kowace wahala a neman zabe, amma da zaran anyi sai kaga wassu dabam ne ke samun mukamai, domin harkar ta koma ta wa Ka Sani a sama,Iya sanin mutanen ka a sama iya samun damar ka ko da kuwa kana kasar waje ne a lokacin zaben.
Abinda shugaban kasa yayi shine ,kirkiran jakadu a jihohin da ba APC ke mulki(Gomna)ba, aikinsu lura da duk aiki gomnatin tarayya da aiwatar da tsare-tsare na Gomnatin kamar a baya lokacin mulkin Shehu Shagari Idan ba haka akayi ba to gaskiya talaka a gaba zasu kaurace ma zaben shugaban kasa domin amfanin sa kadanne a wajensu, A yadda tsarin yake tafiya komai a hanun gwamnoni ake badawa to kaga jihar da bata APC ba jama'ar APC sun koma baya ba moriya.
Zamu hadu a gaba kadan don bayani kan matsalolin APC a matakin kananan hukummomi na jahar Bauchi gwargwadon Sanina da fahimtata sakamakon chudanya, Hulda, da bayanai dana tattara a wajen wasu shugabaninta na kananan hukumomin,Dambam kuwa gida ne.
Na gode sai mun hadu a rubutu na gaba.
Kar ku duk rubutun da Kuga nayi Ina turawa zuwa code na N/East zonal chman da kuma na kasa duk ta code nasu don gaskiya nake fada ba kirkire nakeyi kuma sun Sani Sarai.
Fatan mu ayi gyara,Wallahi na kasa shi yake ganin kura-kurai ,Amma manyan mu a sama bata wannan suke ba, sai dai bukatar Kai ( interest).
Idan Akwai gyara ko shawara Ina maraba dashi akan rubutun don nima har yanzu almajiri ne a fagen siyasa , don har yanzu inada Malamai a siyasance a raye wassu kuma sun mutu( Allah yaji kansu da rahama) misali-:Late. Katukan Misau, Kunce Kura na Bauchi, Shatiman Katagum da Alh. Hassan Sale Giwa (Dallatun Misau na Farko) da sauransu.
A raye kuwa Malamai na sauran hudu(4) ALH Mohd Nadada Umar, Amb.Adamu Jumba sai Alh Mohd Dalko ,sai kuma Littafi daya tilo 48-Laws of Power.
Nagode HON BALA ABDULLAHI (VASCO) Tsohon dan majalisar wakilai Kuma tsohon shugaban jam'iyar APC a karamar hukumar DAMBAM