Dambam Emirate Fcbk Connect

Dambam Emirate Fcbk Connect Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dambam Emirate Fcbk Connect, Media/News Company, Damban.

Dambam Emirate Facebook Connect is a non-profit community-based organization established to promote cultural heritage, peace, youth empowerment, education, humanitarian services, and community development through digital communication and social engagemen

02/09/2026

Assalamu alaikum, jama'a barkanmu da yamma kwana biyu shiru. Muna muku fatan alheri.

Alhamdulillahi Dambam Emirate Fcbk Connect CAC
05/08/2026

Alhamdulillahi Dambam Emirate Fcbk Connect CAC

DAMBAM EMIRATES FACEBOOK CONNECT 2026. FARKONSA DA ABIN DA YA BIYO  BAYAKamar yadda aka sani cewa an gudanar da taron DA...
14/07/2026

DAMBAM EMIRATES FACEBOOK CONNECT 2026.

FARKONSA DA ABIN DA YA BIYO BAYA

Kamar yadda aka sani cewa an gudanar da taron DAMBAM EMIRATE FACEBOOK CONNECT 2026 a wata May da ya gabata, muna mika godiya ta musamman ga daukacin al'ummar Dambam Emirate, musamman wadanda s**a bayar da gudumawar kudi, sayan tickets, shawarwari da sauran nau'ikan tallafi domin ganin an gudanar da taron cikin nasara.

Taron ya samu tagomashi na halartar al'umma kana kuma a wanan karon taron ya samu tallafin kudi daga wadannan al'ummomi

i. Dambam Emirate Council
ii. Sen. Abdul Ahmed Ningi
iii. Hon Ahmed Garba Mohammed
iv. Hon Iliya Isah Dagauda
v. Dr Sani Muhammad Dambam
vi. Hon. Sadiq Tanko Jalam
vii. Hon. Sabo Baffayo Ahmed.
viii. Alh. Abdullahi Babayo Jalam.
ix. Hon. Abdulaziz Muhammad
x. Hon. Abdul Adamu Muhammad (Auduwa Zico)
xi. Shaharuzzaman Nuhu Zaki
xii. Hon. Idris Shehu
xiii. Zaki Media Team
xiii. Hon. Sabo Joji
xiv. Alh. Ishiyaku Sa'idu
xv. Abubakar Idris On top
xvi. Nazif Ali Audu
xvii. Tijjani Abdu Dambam
xviii. Hon. Abdul Adamu
xix. Dr. Abubakar Muhammad Yaya
xx. Hon. Yahaya Yalwa Best.
xxi. Alh. Ahmad Adamu
xxii. Alh Adamu Hamman.

Bayan kammala taron, an samu ragowar wasu kudade daga gudummawar da aka bayar. Kwamitin shirya taron ya ga dacewar kada a bar kudaden ba tare da anfani ba, don haka aka karkata su zuwa ayyukan alheri da s**a amfanar da al'umma kai tsaye.
Daga cikin ayyukan da aka gudanar da wadannan kudade akwai:

1. Yiwa kungiyar Rijista da CAC

2. Bude asusun Banki na kugiya wato Cooperative Account.

3. Tallafin Ilimi;

i. Biya wa dalibi guda Daya kudin registration na Primary School da kayan karatu na tsawon shekara guda.

ii. Daukan nauyin dalibai guda uku (Dambam, Dagauda, Jalam) da sasu a karatun NCE akarkashi NTI study Center ta CAIS Dambam da kuma biya musu kudin registration na Shekara Guda (Session).

Sannan da biyan kudin karatun shekara daya na Yaron marigayi Zahradden Lamara, Allah yaji kansa.

iii. Sayan kayan aiki da tabarmai ga wasu makarantun Islamiyya a kauyukan Dambam.

4. Tallafin Sana'a;

i. Bada tallafin Mai, wake da magi ga Mata masu sana'ar kosai da awara har mutum 31.

ii. Bada tallafin Kwai da Indomi ga masu shayi har mutum 21.

iii. Bada tallafin kudi naira 10, 000 (dubu goma goma,) ga masu kananan sana'oi Mata 10 maza 5 jimla mutum 15.

5. Shirin Free Dental Care domin bai wa jama'a damar samun kulawar lafiyar baki da hakora kyauta wa sama da mutum 250. Wadda masana s**a tabbatar mana cewa kimar aikin in kowa zai biya kudinsa ne ya zarce miliyan daya (₦1m)

Don tabbatar da tsari dukkan wassu da yakamata a basu jadawalin yadda aka kashe kudade da abin da aka Tara mun basu a rubuce, mai Neman karin bayani ya tuntubi shugabanni zai samu dukkan bayanen da yake bukata.

MUNA GODIYA GA DUK MASU BA DA SHAWARA DA KORAFI

Muna mika godiya ga dukkan wadanda s**a kasance tare da mu tun daga farkon shirin Dambam Emirates Facebook Connect 2026 har zuwa bayan kammaluwarsa.

Muna godiya ga wadanda s**a ba mu shawarwari masu amfani, s**a nuna mana hanyoyin gyara da inganta ayyukanmu. Haka kuma muna godiya ga wadanda s**a gabatar da korafe-korafe cikin girmamawa da kyakkyawar niyya domin ganin an gudanar da al'amura yadda ya kamata.

Mun yi nazari a kan dukkan shawarwari da korafe-korafen da muka samu, kuma mun dauki darussa masu yawa daga cikinsu. Wasu daga cikin shawarwarin an aiwatar da su, wasu kuma za su kasance cikin abubuwan da za a yi la'akari da su a shirye-shiryenmu na gaba.

Muna tabbatar wa al'umma cewa manufarmu ita ce hada kan jama'a, bunkasa cigaba, da gudanar da ayyukan alheri ba tare da nuna son kai ko wariya ba. Saboda haka, ba kowane ra'ayi ne za a iya bi nan take ba, muna daraja duk wanda ya ba da lokacinsa wajen bayar da shawara ko gyara.

Muna rokon Allah (SWT) Ya saka wa duk wadanda s**a bayar da gudummawa, masu ba da shawara, masu taimako da masu addu'a da mafificin alkhairi. Allah Ya sanya wannan aiki a ma'aunin kyawawan ayyukanmu Ya kuma ba mu ikon ci gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani al'ummarmu.

Kwamitin Gudanarwa,
Dambam Emirates Facebook Connect 2026.
14/7/2026.

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN...A madadin Dambam Emirate Fcbk Connect muna mika sakon ta'aziyar mu ga iyalen wanann ...
13/07/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN...

A madadin Dambam Emirate Fcbk Connect muna mika sakon ta'aziyar mu ga iyalen wanann mata da Allah ya karba rayuwar ta yau 13/07/2026 ,Yan uwa da abokan arziki da dukkan alummar garin Jalam, Muna rokon Allah ya gafarta mata zunuban ta ya Kuma sa aljanna makomar ta,Muna rokon Allah ya albarkaci abinda ta bari.

Wanann mata ta Kasance daya daga cikin mata da s**a amfana da tallafin da Kungiyar Dambam Emirate Fcbk Connect 2026 s**a gudanar ranan 10/07/2026..

Kwamitin gudanar wa

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un 😭😭 Allah ya yiwa Baba Maibiki Maman Eto'o Rasuwa cikin daran nan. Wannan mata naji r...
13/07/2026

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un 😭😭

Allah ya yiwa Baba Maibiki Maman Eto'o Rasuwa cikin daran nan.
Wannan mata naji rasuwar ta sosai a cikin Raina bisaga dalilai kamar haka. Shekaranjiya Jumu'ah karkashin kungiyar mu ta Dambam Emirate Facebook connect munyi Economic Empowerment, Tallafin mata masu Kananun jari nida kaina nasameta Na sakata cikin su. Saboda sana'arta na suyan kosai a bakin primary school Jalam😭😭

Wallahi kaf cikin matan da muka Sako su ciki inaga Babu Wanda tayi mana Godia tareda fatan Alkhairi da Allah muku Albarka sama daita.🙆🙆
Har a Jalam Saida ta sakemin Godia sosai da sosai
Ko jiya lahdi Ina tsaye a kasuwa tazo tacemin Yarona bani chanjin dubu Daya ko biyar 2 ma. 🤔🤔

Nidai ko alamar zazzabi bangani ba a jikin ta. A jiya Dana Bata chanjin kudi

Irin wannan mutuwa Idan bai girgiza mutum yadawo dashi cikin hankalin shi ba. Inaga har abada mutum bazaiyi hankali da tunani ba wallahi 🤲🤲

Allah ya Miki Rahama Allah yakai haske kabarin ki, Allah yasa chan yafinan gareki
Allah ya sa kina cikin dausayin Aljannah Aameen

Assadeeq Aboubakar 🙏🙏

13/07/2026

A Tribute to the Organizers of Dambam Emirate Facebook Connect

I wish to express my heartfelt appreciation and sincere tribute to the organizers of Dambam Emirate Facebook Connect for their outstanding commitment to serving the people of Dambam Local Government Area without discrimination based on political affiliation, ethnicity, social status, or background.

Your dedication to humanitarian service and community development is truly commendable. Through your selfless efforts, you have positively impacted countless lives by providing free and meaningful support, including:

- Empowerment of Small and Medium-Scale Businesses.
- Support for students through free assistance with NCE admission forms and registration.
- Free dental care services for members of the community.
- Many other humanitarian interventions and community support initiatives that are too numerous to mention.

These remarkable contributions deserve recognition and appreciation from all sons and daughters of Dambam Emirate, development partners, community leaders, and the entire Dambam Local Government Area. Your commitment demonstrates that genuine service to humanity is one of the greatest investments in community development.

Advice to the Organizers of Dambam Emirate Facebook Connect

1. Continue maintaining your excellent record of service and remain committed to improving the lives of the people of Dambam LGA.
2. Strengthen collaboration with sister organizations, especially the Dambam Development Forum, by sharing ideas and working together for the overall progress of Dambam Emirate.
3. Develop sustainable sources of income to support the smooth operation of the organization, as financial sustainability is essential for long-term success.
4. Encourage beneficiaries of your empowerment programmes to establish Village Savings and Loan (VSL) groups where members contribute even ₦1,000 or any affordable amount weekly or monthly. This will create a revolving fund to support members facing financial challenges.
5. Advocate for contributions from influential individuals, traders, transport operators, livestock dealers, business owners, and other well-meaning citizens. Even small regular contributions can collectively provide significant resources to address the needs of vulnerable people in our communities.

Advice to Political Leaders and Influential Personalities in Dambam Emirate

1. Support the Dambam Emirate Facebook Connect initiative because it has demonstrated genuine compassion and commitment to serving the people.
2. Provide every necessary support, including mentorship, security, recognition, encouragement, and moral support to enable the organization to grow.
3. Engage with and encourage the organization regularly. Your guidance and support will inspire them to do even more for the community.
4. The Dambam Emirate should consider organizing a special recognition ceremony to honour the outstanding contributions of the organizers and volunteers whose services deserve public commendation.
5. We call upon all political leaders, traditional leaders, and influential personalities, irrespective of political party affiliation, to unite in supporting this noble initiative for the benefit of the entire Dambam community.

Together, we can build a stronger, healthier, more peaceful, and more prosperous Dambam through unity, compassion, and collective responsibility.

Thank you to the organizers of Dambam Emirate Facebook Connect for your invaluable service to humanity. May Almighty Allah reward your efforts abundantly, strengthen your mission, and grant you greater success in serving our community. Amin.

Tijjani Abdu, RCHP
Community Health Advocate for Resilience and Peace Building

13/07/2026

YANAYIN (HALAYYAR ) KA TUNANIN KA....

GODIYA....

Alhamdulillahi, Alhamdulillahi, Alhamdulillahi Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin Sarki ,wadda ya bamu ikon tsarawa tare da aiwatar da taron Dambam Emirate Fcbk Connect 2026 da Kuma kammala dukkan tsare tsare da aka tanadar don tallafawa al'umma, Bamu ce munfi kowa iyawa ba, Don kasncewar mu Yan Adam masu rauni,cikakken Adalci na Allah ne shi kadai ke iyawa kowa, Munyi iya Abinda zamu iya Muna rokon Allah ya bamu ladan wannan aiki,ya Kuma yafe mana Kura kurai da muka aiwatar..

TSOKACI....
GA duk wadda ya fahinci rayuwa zaiga cewa mutane Azzalumai akoda yaushe tunanin su akan mutane shine zasu zalinci,Mutane mungaye wadda zuciyar su Babu Alkairi acikin ta Koda yaushe haka suke munana tunanin su ga sauran mutane, haka zalika maciya Amana s**an kasance cikin tunanin kowa ma haka yake mu analantar sauran al'umma...wanann shi ake nufi da yanayin ka tunanin ka...Ya Allah ka Kare mu daga Zalinci,Cin Amana da tunanin mun fi kowa iyawa,Ya Allah mu masu rauni ne Kar kabar mu da iyawar mu....

NASARA.,..

Wannan taro ya kasance nasara da Kuma zama abin tunawa da alfahari dashi ga wanann masarauta tamu me albarka,tarihi ne da aka rubuta shi da tawadar zinare,Kuma abin koyi ga na baya.

A kalla al'umma sun anfana ta Hanyoyi da yawa kamar...

1. Biyawa a kalla mutane hudu kudin karatun shekara guda don samun shaidar karatun NCE ,Wadda dukkan su masu hidimtawa al'umma ne a makarantu ba tare da sun mallaki shaidar karatun NCE ba...
2. Tallafawa maza da mata masu kananan sana'a a kalla 56 da kayayyaki kamar kudi,Indomie,Kwai(eggs) mangyada,Maggi da wake..
3. Aikin lafiya (Hakori) a kalla a mutane 300 wadda ya shafi cire Hakori,cikewa,saka sabon Hakori,wanke hakora da sauran su.
4. Samar da register (CAC) da asusu GA wannan kungiya wadda cikin kankanin lokaci Insha Allah zai shiga hanu..

Muna rokon Allah ya sa wannan aiki a mizanin mu,Allah ya sakawa dukkan wadanda s**a tallafa da kudi gudumawa,da dukkan wata hanya don gudanar wannan taro ,tabbas badon ku ba da ba a samu wannan nasara ba..

Mun gode ,Allah yasa Muna raye shekara Mai zuwa don gudanar da taro na gaba..

Kwamitin Gudanar wa..

Together we write History...Some of Our team Members for the .Dambam Emirate Fcbk Connect 2026 Free Dental Services
12/07/2026

Together we write History...Some of Our team Members for the .Dambam Emirate Fcbk Connect 2026 Free Dental Services

12/07/2026

Alhamdulillahi Done and Dusted... Economic Empowerment , Free Dental Services and 80% of Educational Sponsorship..It's indeed a success.

SAƘON GODIYA DA  JINJINA....A Madadin  MAI MARTABA SARKIN DAMBAM ALH IDRIS MUSA SULAIMAN da masarautar Dambam Mai albark...
12/07/2026

SAƘON GODIYA DA JINJINA....

A Madadin MAI MARTABA SARKIN DAMBAM ALH IDRIS MUSA SULAIMAN da masarautar Dambam Mai albarka,kwamitin gudanar wa, da sauran kananan kwamitoci na kungiyar DAMBAM EMIRATE FACEBOOK CONNECT 2026 da daukacin al'ummar da s**a amfana da AIKIN HAKORI KYAUTA tsawon kwana biyu ( Two days free dental services)Muna Mika sakon godiya da Jinjina marar iyaka ga jajirtattun likitocin mu (Dental Technicians ) wadda s**a gudanar da wannan aiki, Allah ya kara hada kanmu ya mana albarka baki daya, marasa lafiya kuma Allah ya basu lafiya....

A lokacin gudanar da wanann aiki mun samu ziyarar karfafawa da Kuma sanya albarka a wannan aiki daga mai girma kwamishinan Lafiya na Jihar Bauchi DR SANI MUHAMMED DAMBAM.

12/07/2026

Address

Damban

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dambam Emirate Fcbk Connect posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share