29/04/2025
AN KADDAMAR DA LITTAFIN “RAYUWATA” A ABUJA
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Ranar Asabar 28 ga Shawwal 1446 (26/4/2026) aka kaddamar da littafin tarihin Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda ya bayar da kansa mai suna “RAYUWATA”.
A yayin jawabinsa a wajen taron, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa: “Na fadi wani abu a takaice (a gabatarwan littafin), cewa, wannan littafi sakamako ne na tunani da ya zo mana da muke tsare bayan waki’ar da aka sanya ma suna waki’ar Buhari, sai muka ga Allah Ta’ala ya bar mu da rai, tunda sun zo kisa ne kawai, ba yadda za a ce ma an rayu a wannan hali, amma dai da yake Allah ne me raya wa. Kamar yadda nace, Allah da ya kai Musa (AS) hannun Fir’auna, ya raine shi, sai ya kai mu hannunsu kuma, suna so su kashe amma kuma sai suna kula da mu.
“Sai muka ga to tunda dama ta samu, bari mu fadi wani abu wanda watakila in ba mu muka fada ba ba za a sani ba. Ita Malama sai ta yi rubutu; ita ta rubuta ne, ta saka da Ingilishi ‘A brief history of the Islamic movement.’ Ni kuma sai na yi bayani da baki, ina fada tana sajjalawa, muna yi kamar muna magana ne, kamar ma tana min tambayoyi ne ina amsawa, sai dai da aka rubuta littafin ba a sa tambaoyin nata ba, sai aka mai da shi littafi. Amma kamar muna magana ne, idan mutum ya saurari sautin zai ji muna magana ne.” Inji Jagora.
Ya kara da cewa: “Kusan duk abin da na fada duk a takaice ne kuma a gurguje, domin kowane bangare na rayuwar zai zama akwai magana mai tsawo wanda shi kansa zai iya zama littafi. Alal misali, da zan ce zan bayar da labarin karatuna na zaure ne kawai, to ai zan yi littafi ne, amma kawai sai na fada a gurguje kawai. Haka karatun nizamiyya, shima zai iya zama littafi, amma shima sai ya tafi a gurguje. Kuma gidajen yari kowanne littafi ne.”
Shaikh Zakzaky ya yi tsokaci akan wasu daga kusa-kuran da aka samu daga aikin rubuta littafin daga ‘audio’ din bayanan, kamar amfani da kalmar ‘na yi’ maimakon ‘in yi’, da kuma yadda aka rubuta sunayen wasu m