Danja Pulse

Danja Pulse Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Danja Pulse, Media/News Company, Danja.

BARKANMU DA ZUWA DANJA PULSE

First for Danja – Gaskiyar Labari

Muna kawo muku:
📰 Sahihan labaran Danja
📢 Muhimman sanarwa
🎉 Shirye-shirye da events
📸 Hotuna da bidiyo

Ku turo mana domin yadawa!
📩 DM ko WhatsApp: 09068626703

APC Ta Tsayar Da AB Dabai A Matsayin Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Ta Bakori Da Danja Jam’iyyar APC ta tsayar da AB Daba...
16/05/2026

APC Ta Tsayar Da AB Dabai A Matsayin Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Ta Bakori Da Danja

Jam’iyyar APC ta tsayar da AB Dabai a matsayin ɗan takararta na kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Bakori da Danja, bayan cimma matsayar sulhu tsakanin masu neman tikitin jam’iyyar.
An tabbatar da hakan ne bayan sauran masu neman takarar sun janye domin bai wa AB Dabai damar zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027 mai zuwa.
Rahotanni sun ce an gudanar da tsarin tabbatar da zaɓen ne bisa tanadin doka tare da sa ido daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki.
Jam’iyyar ta yaba wa masu neman takarar da s**a amince da matsayar da aka cimma, tana mai cewa matakin zai ƙara ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin mambobinta.
APC ta kuma yi kira ga dukkanin ’ya’yanta da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a babban zaɓe mai zuwa.
Daga cikin waɗanda jam’iyyar ta yaba wa gudunmawarsu akwai Yakubu Nuhu Danja da Yusuf Muhammad Jika da kuma Shehu Dabo Dabai.
Jam’iyyar ta yi musu fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya ba AB Dabai nasara a zaɓen da ke tafe.

A Gurin Allah Muke Nema — Al'ummar Ɗanja Sun Yi Wa Dan Takarar Majalisar Jiha Na Karamar Hukumar Danja A Tutar Jam'iyar ...
11/05/2026

A Gurin Allah Muke Nema — Al'ummar Ɗanja Sun Yi Wa Dan Takarar Majalisar Jiha Na Karamar Hukumar Danja A Tutar Jam'iyar Adc, Hon. Abdul’aziz Mustapha Dan Audu Danja Kyakkyawar Tarba Tare Da Nuna Goyon Bayansu A Kansa

A jiya Lahadi 10/05/2026 ne ɗan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Danja a ƙarƙashin jam’iyar ADC, Hon. Abdul’aziz Mustapha Dan Audu Danja, ya ƙaddamar da takararsa a hukumance bayan al'ummar danja sun hada kudi da kansu sun kammala siya mai fom ɗin tsayawa takara domin fafutukar ceto al’ummar Danja daga matsalolin rashin ingantaccen wakilci na gari.

A jawabinsa yayin taron ƙaddamarwar, Hon. Abdul’aziz Mustapha Dan Audu ya bayyana cewa:

Mun fito wannan takara ne don amsa kiran al'ummar karamar hukumar danja
“Ba don son rai ko neman mulki kawai muka yadda muka amince muka fito wannan takara ba, mun fito ne saboda kiraye-kirayen al’umma daga kowane lungu da saƙo na ƙaramar hukumar mu tare da yakinin idan Allah ya bamu nasara zamu sharewa al'ummar danja hawaye.

Al’umma sun gaji da zama yan kallo, sun gaji da wakilcin da bai amfani jama’a ba sun gaji da cewa lallai wata miyar sai a makota. Lokaci ya yi da mutanan danja zasu samu wakilci na gari insha Allahu.”

Ya ƙara da cewa:

“Mun ga irin koma bayan da ƙaramar hukumar Danja ke fuskanta ta fuskar ci gaba, matasa da mata na fama da rashin aikin yi, hanyoyi sun lalace, ilimi ya gurbace idan aka dawo bangaren lafiya kuma sai innah lillahi wa innah ilaihir raji'un domin mutanan karamar hukumar danja na cikin mawuyacin hali a wannan bangaren. Wannan ne yasa muka amsa kiran jama’a domin mu fito mu kawo sauyi na gaskiya.

Da yardar Allah, Danja zata samu wakilcin da zai ɗaga martabar al’umma ba wai anfani na kai da kai ba.”

Taron ƙaddamarwar ya samu halartar dubban jama’a daga kowane yanki na mazabu goma (10) dake faɗin ƙaramar hukumar Danja, sun tabbatar ma duniya cewa su s**a aminta da wannan takara, kuma jam'iyar ADC na samun karin karɓuwa da farin jinin Hon. Dan Audu Danja ne a tsakanin al’umma musamman matasa da mata masu kishin cigaban Danja.
Bayan kammala taron, Hon. Dan Audu Danja tare da tawagarsa sun kai ziyarar girmamawa ga magabata da dattawan gari domin neman albarka, addu’a da shawarwari kan wannan tafiya ta siyasa.

Inda ya bayyana musu cewa:
“Mun zo ne domin neman goyon baya da addu’ar ku. Wannan tafiya ba ta mutum ɗaya ba ce, tafiya ce ta al’ummar Danja baki ɗaya. Muna neman haɗin kan kowa da kowa domin ceto ƙaramar hukumar mu daga durƙushewar cigaba.

”Daga cikin manyan baƙin da s**a halarci taron akwai:

*Hon. Barr. Usman Buhari Umar Danja
*Hon. Nasiru Bawale
Hon. Sa’idu Yahaya Yassah
*Amb. Abu Bako Dabai
*Shugabannin jam’iyar ADC na ƙaramar hukuma da mazabu
*Shugabannin ƙungiyoyin matasa na jam’iyar ADC
*Shugabannin kungiyoyin mata na jam'iyar ADC
Da sauran masu ruwa da tsaki na cigaban ƙaramar hukumar Danja

A jawabin wasu Daga cikin , ƙungiyoyin matasan na jam’iyar ADC sun yi kira ga dukkan stakeholders, dattawa, masu ruwa da tsaki da al’ummar Danja da su mara wa Hon. Abdul’aziz Mustapha Dan Audu baya domin shi ne ya cancanta duba da yadda mutane s**a fito s**ayi dafifi wajan tar barshi a cikin garin dabai da danja lokacin daya kai ziyara wajan iya yen kasa.
Sannan Sun bayyana cewa:

“Hon. Dan Audu mutum ne mai nagarta, hangen nesa, tausayi da kishin talaka. Yana da dukkan qualities da ake nema ga shugaba na gari. Matasa suna tare da shi da Mata, al’umma suna tare da shi, kuma da yardar Allah nasara tamu ce.”
Danja na neman sauyi…
Danja na neman wakilci nagari…
Danja na neman shugaba mai kishin talaka…
Kuma da yardar Allah, Hon. Abdul’aziz Mustapha Dan Audu Danja shine mafitar al'ummar don yanzu ne akasa kwarya a gurbin ta!

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Katsina, na sanar da ɗaukacin maniyyatan aikin Hajjin Bana (2026) da s**a fito daga w...
09/05/2026

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Katsina, na sanar da ɗaukacin maniyyatan aikin Hajjin Bana (2026) da s**a fito daga waɗan nan ƙananan hukumomin; BAKORI, DANDUME, DANJA, FASKARI, FUNTUA DA SABUWA, da su hallara sansanin Alhazan na jihar Katsina a gobe Lahadi da misalin ƙarfe 11 na safe, domin fara shirye-shiryen su na tafiya ƙasa mai tsarki.

Cibiyar CDA Dake a Jami’ar Bayero Kano Hadin Gwiwa Da Hukumar Inganta Noman Rani Ta Jihar Katsina Sun Shirya Horo Na Kwa...
08/05/2026

Cibiyar CDA Dake a Jami’ar Bayero Kano Hadin Gwiwa Da Hukumar Inganta Noman Rani Ta Jihar Katsina Sun Shirya Horo Na Kwana Biyar Ga Ma’aikatan KTIDA Domin Bunkasa Noman Rani Da Kawo Sabbin Dabarun Noman a Katsina

Cibiyar Bincike Kan Noma a Busassun Yankunan (CDA) ta jami’ar Bayero Kano hadin gwiwa da hukumar KTIDA Katsina sun shirya horo na kwana biyar ga ma’aikatan KTIDA musamman a bangarorin da s**a shafi Micro-Irrigation da kuma dabarun noma da s**a dace da sauyin yanayi.

Taron ya mayar da hankali ne wajen kara wa ma’aikatan Hukumar KTIDA ilimi da kwarewa a kan hanyoyin zamani na amfani da ruwa wajen noma, musamman tsarin micro-irrigation wanda ke taimakawa wajen rage asarar ruwa tare da kara yawan amfanin gona.

Haka kuma, horon ya mayar da hankali kan dabarun noma masu dacewa da sauyin yanayi (Climate-Smart Agriculture), domin taimaka wa manoma da hukumomin noma wajen tinkarar matsalolin sauyin yanayi da ke barazana ga harkar noma a yankuna masu fama da karancin ruwa.

Masu horaswar daga Cibiyar CDA ta Jami’ar Bayero Kano sun gabatar da darussa kan yadda za a yi amfani da sabbin hanyoyin ban ruwa, kula da albarkatun kasa da ruwa, da kuma dabarun inganta noman rani cikin sauki da inganci.

Jami’an Hukumar KTIDA da s**a halarci horon karkashin jagorancin Eng. Saleem Sulaiman sun bayyana jin dadinsu tare da yabawa gwamnatin jihar Katsina da cibiyar CDA bisa samar da wannan dama ta kara musu ilimi da kwarewa domin bunkasa harkar noma ta ruwa a jihar.

Taron yana gudana ne daga ranar Alhamis 7 ga watan Maris zuwa 11 ga watan Maris a dakin taro na CDA dake a jami’ar Bayero a jihar Kano.

Gwamna Raɗɗa Ya Kaddamar da Motoci ga Hukumar KASSAROTA Domin Inganta Tsaron Hanya a KatsinaGwamnan Jihar Dikko Malam Di...
07/05/2026

Gwamna Raɗɗa Ya Kaddamar da Motoci ga Hukumar KASSAROTA Domin Inganta Tsaron Hanya a Katsina

Gwamnan Jihar Dikko Malam Dikko Umar Radda, a ranar Alhamis, ya kaddamar da motoci ada gwamnatin jihar Katsina ta samar wa Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA), domin kara inganta ayyukan kula da zirga-zirga da tsaron hanya a fadin jihar.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a harabar gidan gwamnatin jihar Katsina Muhammadu Buhari House.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumar KASSAROTA karkashin jagorancin babban daraktan Hukumar Manjo Garba Yahaya Rimi, mai ritaya, da babban kwamandan hukumar Dahiru Mani Bagiwa (rtd) da sauran jami’an hukumar.

Da yake jawabi yayin kaddamarwar, Gwamna Raɗɗa ya ce samar da motocin aikin na daga cikin kudurin gwamnatinsa na inganta tsaron hanya, kula da zirga-zirga da kuma ayyukan ceto a fadin jihar.

Ya bayyana cewa motocin za su taimaka wajen kara wa jami’an KASSAROTA karfin gudanar da ayyukansu, musamman wajen tabbatar da bin dokokin hanya, dakile hatsurran mota da kuma saurin kai dauki a lokuta daban-daban.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin ingantaccen tsarin kula da zirga-zirga wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da bunkasa harkokin tattalin arziki da zamantakewa.

Raɗɗa ya kuma yaba wa jami’an KASSAROTA bisa jajircewarsu wajen gudanar da aiki, tare da kira gare su da su ci gaba da nuna kwarewa, da’a da adalci yayin gudanar da ayyukansu.

Ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa hukumomin da ke kula da tsaro da zaman lafiya ta hanyar samar musu da kayan aiki da sauran bukatun gudanarwa.

A nashi jawabin, shugaban hukumar KASSAROTA ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, yana mai bayyana motocin a matsayin babban ci gaba ga ayyukan hukumar.

Rimi ya kuma yi alkawarin kara kaimi wajen wayar da kan jama’a kan tsaron hanya, inganta kula da zirga-zirga da kuma kare masu amfani da hanyoyi a fadin jihar.

07/05/2026

Kawo mana Unguwa daya Da kasani Cikin Garin Danja

06/05/2026

MUNA MUKU BARKA DA WANNAN LOKACIN

Matasan jihar Katsina su shar; Gwamnatin Katsina Ta Tallafa Da Naira Miliyan 50, A Lokacin Fara Shirin Horar Da Matasa 5...
06/05/2026

Matasan jihar Katsina su shar; Gwamnatin Katsina Ta Tallafa Da Naira Miliyan 50, A Lokacin Fara Shirin Horar Da Matasa 500 Sana’o’in Hannu

A ranar Laraba, 6 ga watan Mayun 2026, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya halarci bikin yaye matasa 500 da s**a kammala horo kan sana’o’in hannu daban-daban na tsawon wata biyu. Shirin, wanda tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc Ahmad Musa Dangiwa, ya shirya, ya gudana ƙarƙashin haɗin gwiwar Family Homes Fund da Bankin Raya Afirka (African Development Bank).

A yayin bikin, Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana bayar da tallafin Naira miliyan 50 a lokacin fara shirin domin ƙara ƙarfafa shirin da tabbatar da nasarar sa a tsakanin matasa.

Da yake jawabi, Arc Ahmad Musa Dangiwa ya bayyana cewa an zaɓi matasan ne ta hanyar shugabannin ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina, domin tabbatar da adalci, gaskiya da daidaito wajen shigar da wanda za su amfana da shirin.

Ya ƙara da cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa matasa su dogara da kansu ta hanyar koyon sana’o’in da za su zama hanyar samun abin dogaro da kai, maimakon jira aikin gwamnati kaɗai.

A wajen taron, an kuma karrama matasa biyu, mace da namiji da s**a fi ƙwazo na kowane fanni cikin fannoni shida da aka horas da kyautar Naira 250,000 kowanne, a matsayin karfafa guiwar ƙwazon da s**a nuna a lokacin horon.

Bayan kammala shirin, an raba wa dukkan matasan kayan fara sana’a. Sana’o’in da aka koya musu sun haɗa da fenti, kafinta, gyaran lantarki, aikin famfo (plumbing) da sauran sana’o’in hannu.

A nasa jawabin, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya jaddada cewa gwamnatin sa ta mayar da hankali sosai wajen bunƙasa matasa ta hanyar basu ƙwarewa da damar dogaro da kai.

Ya bayyana “Muna son matasan mu su zama masu samar da ayyukan yi, ba masu neman aiki kawai ba. Wannan gwamnati za ta ci gaba da buɗe musu ƙofofin dama a dukkan fannoni na rayuwa. Duk inda aka samu aikin gwamnati, za mu tabbatar matasan mu sun taka rawar gani.”

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati za ta haɗa waɗannan matasa da masu kwangilar ayyukan gwamnati domin su samu damar aiki da amfani da horon da s**a samu.

Haka kuma, ya bayyana cewa za a ci gaba da amfani da su a manyan ayyukan gine-ginen gidaje da za a gudanar a Kankia da Radda, domin ƙara samar da ayyukan yi da inganta rayuwar jama’a a jihar Katsina.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

May 6, 2026.

05/05/2026

BARKANMU DA ZUWA DANJA PULSE

First for Danja – Gaskiyar Labari

Muna kawo muku:
📰 Sahihan labaran Danja
📢 Muhimman sanarwa
🎉 Shirye-shirye da events
📸 Hotuna da bidiyo

👉 Kuna da labari ko event?
Ku turo mana domin yadawa!

📩 DM ko WhatsApp: 09068616703

Danja Pulse – First for Danja

Address

Danja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Danja Pulse posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share