
17/03/2025
Zaben 2027: Haɗakar Bala Mohammed Da Peter Obi Nasarace Ga Al'ummar Najeriya
Kungiyar Matasa ta Yankin Neja Delta (NDYC) ta jinjinawa hadin gwiwar Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, wanda kuma shi ne Shugaban Gwamnonin PDP, da tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi. Kungiyar ta bayyana haduwar su a matsayin matakin da zai kawo sauyi a siyasar Najeriya, domin yana dogara ne akan juna, kishin kasa, da hangen nesa na ci gaba.
A wannan lokaci da ‘yan Najeriya ke bukatar jagoranci na gari da ke kula da bukatun al’umma, Bala Mohammed da Peter Obi sun zama sabbin shugabanni da za su iya kawo sauyi. Bala Mohammed ya nuna jajircewarsa wajen hadin kan kasa da gina manyan ababen more rayuwa, yayin da Peter Obi kuma ke da suna wajen ingantaccen shugabanci da sarrafa tattalin arziki cikin gaskiya. Hadin gwiwarsu alama ce dake nuna cewa siyasa ta Najeriya na tunkarar sabon salo na gaskiya da ci gaba.
NDYC ta kwatanta wannan sabon salon siyasa da tsoffin 'yan siyasa kamar Atiku Abubakar, wadanda ke makale cikin tsarin siyasar da ke da alaka da son zuciya. Sabanin irin wadannan ‘yan siyasa da ke kokarin hawa mulki don biyan bukatun kansu, Bala Mohammed da Peter Obi suna wakiltar shugabancin da ke mayar da hankali kan gaskiya, nagarta, da ci gaban kasa.
Kungiyar ta jaddada irin nasarorin da Bala Mohammed ya samu a Bauchi, musamman a bangaren ilimi, kiwon lafiya, da gyaran birane, wanda ya nuna cewa yana da kwarewar tafiyar da gwamnati. Haka kuma, irin salon tafiyar da mulki na Peter Obi a jihar Anambra alama ce ta shugabanci mai inganci da dogaro da tattalin arziki mai dorewa. Idan aka hada karfin su a 2027, Najeriya na iya samun gagarumin ci gaba.
NDYC ta bukaci dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa, musamman matasa, da su goyi bayan wannan hadin gwiwa domin tabbatar da cewa 2027 ba zai zama shekarar sake maimaita tsoffin ‘yan siyasa ba, sai dai shekarar da za a fara sabon salo na shugabanci nagari. Kungiyar ta bayyana cewa zamanin siyasar da ke cike da kage da lalacewa ya kare yanzu lokaci ne na shugabanci na gari, gaskiya, da sakamako mai kyau ga al’umma.
SIGNED
Comrade Israel Uwejeyan
National Coordinator, Niger Delta Youth Congress (NDYC)