SABIU Abubakar Gwanda Rimaye

  • Home
  • SABIU Abubakar Gwanda Rimaye

SABIU Abubakar Gwanda Rimaye Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from SABIU Abubakar Gwanda Rimaye, Rimaye kankia, .

15/05/2026

"Ɓoye Sirrin Ɗan Uwanka Ibadah Ne, Kyautata Masa Zato Wajibi Ne, Bin Diddiginsa Haramun Ne...!"

__Imam Ali {AS}
💔🌹

15/05/2026

Namiji kamar shinkafar hausa yake... duk yadda kika kai da tsinceta Sai kin ga tsakuwa a cikin ta, ita mace kuma kamar taliyar hausa ce, duk yadda takai da iya girki, sai ta cabe, dan haka sai muyi hakuri da juna akar6a da hakuri asarrafa abinda yasamu.

15/03/2026

Congratulations to the Ummah.

Netanyahu's death has been confirmed.

15/03/2026

*“Duk wanda yayi karatun Addini kuma bai zama mutumin kirki ba, ya yi asarar lokacinsa.”*

24/12/2025

Ka Himmatu Wajan Neman
Ilimin Addini da Aiki da Shi
- Sheikh Ibraheem Zakzaky

Allahu AkbarRayuwa kenan babu Baban sa babu shima MalamYau Lahadi 15/12/2024 - 14 J/Sani 1446  Kwanaki 138 babu Almarhum...
15/12/2024

Allahu Akbar
Rayuwa kenan babu Baban sa babu shima Malam
Yau Lahadi 15/12/2024 - 14 J/Sani 1446 Kwanaki 138 babu Almarhum Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos (رحمه الله)

Gaskiya kafin rabuwar sa da Mahaifin sa akwai babban soyayya da tausayi da jin kai uwa uba akwai biyayya

Malam Adamu Tsoho ba shine yaro na farko a wajen Mahaifin su ba amma ya sami sheda na girma.

Allah ka jikan su da Rahama domin Annabi Rahama Muhammad (s.a.w.w)

25/11/2024

WAFATIN SAYYID AL-ƘASIM ƊAN IMAM MUSAL KAZIM KUMA ƊAN UWAN IMAM ALI AL- RIDHA (A.S)

Sayyid Ƙasim ɗan Imam Musal Kazim (a.s.) ya yi wafati a irin wannan rana ta 22 ga watan Jumadhal Ula cikin shekara ta192 daga hijirar kakan sa Annabi (saww) a wata riwayar , wanda aka binneshi a jihar Hilla (Babila) dake ƙasar Iraƙi .

TAƘAITACCEN TARIHIN SA

Sunansa Al-ƙasim ɗa ne ga limami na bakwai daga jerin limaman shiriya watau Imam Musal Kazim (a.s.) kuma shine autan ƴaƴan sa , an haifeshi a shekara ta 150 daga hijirar Annabi (saww) a birnin Madina mai tsarki , Imam Musal Kazim (a.s) ya kasance yana matuƙar kaunar Al-ƙasim har yana faɗa yana cewa a wani Hadisi :
Da ace Al'amari a hannuna yake (zaɓar Imami) da na sanya Alƙasim shine Imami a bayana saboda so da ƙaunar da nake masa sai dai lamarin a hannun Allah yake shine yake zaɓar inda zai sanya shi .

Lokacin da Daular Banul Abbasiyyawa s**a matsawa Sharifai Alawiyyawa da kisa da zalunci da danniya har takai ga Harunurrashid (L)yana yanke hannun ƴa-ƴan Nana Faɗima (a.s.) da sauran nau'in uƙubobi ya tarwatsa su a Duniya , daga cikin waɗanda s**a gudu akwai Sayyid Al-ƙasim ɗan Imam Musal Kazim (a.s.) , ya gudu daga gida yabi gefen kogin furatu yana tafiya saboda yasan akwai kakan sa Imam Ali (a s.) a wannan yankin (Najaf) , yana cikin tafiya a gefen kogin Furatu sai ya ga wasu yara mata su biyu suna wasan ƙasa ɗaya tana magana da ƴar uwarta tana cewa :
Ba haka bane na rantse da Ma'abocin bai'ar Ghadir (Imam Ali) ɗayar kuma tana bata haƙuri , da yaji haka sai yace mata : Wa k**e nufi da wannan maganar ? Sai tace masa : Mai s**a da takobi biyu da mashi biyu Baban Hasan da Husain , sai yace mata : Ya ke ƴata ko za ki kaini wajen mai wannan unguwar taku ? Sai tace masa : Ai shine Mahaifina , sai ta shiga gaba ya bita a baya har s**a isa gidan su wajen mahaifin su kuma tayi masa iso , aka saukeshi a gidansu tsawon kwana uku kamar yadda yake a al'adar larabawa s**an yi kwanaki uku da baƙo kafin ma su tambaye shi daga ina yake

23/11/2024
BORE SHI NE KAWAI MAFITA A NAJERIYA____Shaikh Ibraheem Yaqoub  Zakzaky (H). "Abin da ke gaban mu shi ne bore na bamu yar...
03/11/2024

BORE SHI NE KAWAI MAFITA A NAJERIYA

____Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H).

"Abin da ke gaban mu shi ne bore na bamu yarda ba! Ni ban san har wani lokaci za a kai ba, komai akai ma mutane su yi shiru, an dauke wuta ana fama da zafi, su ce kaga tsinannun nan basu kawo wuta ba ko? Shikenan. Ka ga shegun nan basu kawo ruwa ba, tsinannu.

Zuwa can in an kawo, mutane su ce kaga ma ta6o s**a turo mana. Shikenan ya zauna shiru.

Ana nan rashin lafiya ya same shi ya je asibiti ya wuni ba a duba shi ba, ko an zurma masa allura ciwo ya karu, ace magani ya kare. Sai dai ace kaga wadannan dai yadda s**a kashe wane, Allah dai ya isa, shikenan.

Anya haka za a ci gaba? Su wadannan Azzaluman an fada muku haka ya dame su ne? In dai za ku zauna ku yi shiru, to kuwa za a ci gaba.

Abin da ke gaban mu bore ne na bamu yarda ba! Har sai sun ga uwar bari! Ba kuma wai su gyaru ne ba, a'a har kowane tsinanne ya san mafitarsa, ya haura katanga! In tsinanne ya ji an kewaye gidansa ya ce akwai hanyar fita? Aka ce ai ba kofa ta baya, sai ya haura katanga.

Shine kawai. Kuma ko an ki ko an so, abin da zai fitar da mu kenan. Ba wata hanya!

~Sayyid Ibraheem Zakzaky (H). a wajen rufe Muzaharar Maulud
2007.

© Tafsir da jawaban Jagora

Address

Rimaye Kankia

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SABIU Abubakar Gwanda Rimaye posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share