Mujallar Hikima TV

  • Home
  • Mujallar Hikima TV

Mujallar Hikima TV Mujallar Hikima is an intellectual and analytical publication dedicated to philosophy, thought, culture, and critical discourse. MURYAR HIKIMA, MADUBIN GASKIYA.

It is published under Wisdom Production, a registered media and creative enterprise.

"Ana yaƙar arewa ta fuskoki uku, amma mutanen yankin sun gaza ganewa." In ji Shaikh Ibrahim Zakzaky1. Ta fuskacin Noma: ...
08/05/2026

"Ana yaƙar arewa ta fuskoki uku, amma mutanen yankin sun gaza ganewa." In ji Shaikh Ibrahim Zakzaky

1. Ta fuskacin Noma: wadda ita ce tushen arziƙin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an kore su daga garuruwansu, wanda ya zauna za a kashe shi.

2. Ta fuskacin Kiwo: Makiyaya an daɗe ana kwashe dabbobin su. Sannan kuma an yi amfani da wannan damar wajen ƙirƙirar faɗan makiyaya da manoma.

3. Ta fuskacin Kasuwanci. Sufurin kayayyaki ya zama haɗari, saboda ayyukan ƴan-ta'adda a hanyoyi. Sai gobara a kasuwanni wadda ba ta lafiya bace, an rasa me ke haddasa ta. Ɗan-kasuwa idan yabi hanya a sace shi a nemi kuɗin fansa, sai dai a kwashe jarinsa a fanso shi ya dawo ba abin juyawa.

Su kuma manyan yankin ba wannan ne ya dame su ba, in dai za a ba mutum muƙami shikenan kawai.

© Mujallar Hikima TV

Daga ajiye karatu zuwa jagoranci—tafiyar siyasa ba koyaushe take bin hanyar da aka saba gani ba.Yayin da Vijay ke tasowa...
05/05/2026

Daga ajiye karatu zuwa jagoranci—tafiyar siyasa ba koyaushe take bin hanyar da aka saba gani ba.

Yayin da Vijay ke tasowa a siyasar Tamil Nadu, tambayar da ta tsaya a zukatan al'umma ita ce:
shin takardar shaida ce ke gina shugaba, ko hangen nesa da goyon bayan jama’a?

Mujallar Hikima TV
Muryar Hikima, Madubin Gaskiya

Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami, ya ƙi amincewa da zaɓe...
04/05/2026

Ɗaya daga cikin masu neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Pantami, ya ƙi amincewa da zaɓen Jamilu Isyaku Gwamna a matsayin ɗan-takarar gwamnan jihar ta hanyar sulhu (consensus candidate).

Wannan mataki na iya haifar da sabon salo na taƙaddama a cikin jam’iyyar gabanin zaɓe.

Shin wannan rikici zai raba kan jam’iyya, ko kuwa za a samu maslaha kafin zaɓe?

© Mujallar Hikima TV

Iran na nazarin martanin Amurka kan sabon shirin tattaunawa da aka gabatar a rubuce.•Rahotanni sun dogara da tsohon shir...
03/05/2026

Iran na nazarin martanin Amurka kan sabon shirin tattaunawa da aka gabatar a rubuce.

•Rahotanni sun dogara da tsohon shiri na kwanaki 20 da s**a wuce—wanda an riga an sauya shi zuwa yanzu.

•Amurka ta sabunta nata shirin sau uku.

•Iran ta gabatar da sabon tsarin makala-14 da ke fayyace ‘Jajayen Layinta’.

•Sabon shirin Iran bai ƙunshi dakatar da tace uranium na shekaru 15 ko buɗe Hurmuz ba.

Shin wannan tattaunawa za ta kai ga sulhu, ko za ta ƙara zurfafa rashin amincewa?

© Mujallar Hikima TV

A cikin ƴan-gwagwarmaya 175 da Isra’ila ta cafke yayin yunƙurin kai agaji zuwa Gaza, yawancinsu an sake su, amma Saif Ab...
03/05/2026

A cikin ƴan-gwagwarmaya 175 da Isra’ila ta cafke yayin yunƙurin kai agaji zuwa Gaza, yawancinsu an sake su, amma Saif Abu Keshek da Thiago Ávila har yanzu suna tsare.

Shin taimako laifi ne, ko tsarin duniya (world order) ne ke tsoron jinƙai?

© Mujallar Hikima

03/05/2026

Za mu ci'gaba da kawo muku labarai da rahotanni daga wannan shafi na Mujallar Hikima.

29/04/2026
IRAN TA ZAMA GAGARABADAU A YANKIN GABAS TA TSAKIYA, TA SHIGA SAHUN ƘASASHE MAFIYA ƘARFI A DUNIYADaga yin gargaɗi har Amu...
16/01/2026

IRAN TA ZAMA GAGARABADAU A YANKIN GABAS TA TSAKIYA, TA SHIGA SAHUN ƘASASHE MAFIYA ƘARFI A DUNIYA

Daga yin gargaɗi har Amurka da Birtaniya sun fara kwashe sojoji da ma’aikatansu daga yankin

A siyasar duniya, ba kowane iko ake auna shi da yawan mak**ai ko girman tattalin arziƙi kaɗai ba. Akwai ikon da ke bayyana kansa ne ta hanyar tasiri, tsayayyen tsari, da ikon tilasta wa manyan ƙasashe su sake lissafi. A wannan ma’auni ne Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai wani matsayi da tarihi ba zai iya mantawa da shi ba, matsayin da ya sanya ta zama gagarabadon ƙarfi a Gabas ta Tsakiya, har ma ta shiga sahun ƙasashen da ake lissafawa masu ƙarfi a matakin duniya.

Gargaɗin da Iran ke yi ga Amurka a yau ba a kan harshe kawai ba ne. Gargaɗi ne da ke ɗauke da tasirin gwagwarmaya, tsayayyen tsari mai cike da juriya, da ikon yin tasiri ta hanyoyi daban-daban, k**a daga soja, siyasa, da kuma addini. Wannan ne ya sa, a karon farko cikin dogon lokaci, manyan ƙasashen yamma k**ar Amurka da Birtaniya s**a fara ɗaukar matakan kariya, ciki har da kwashe wasu sojoji da ma’aikatansu daga yankin, ba don an fara yaƙi ba, sai don yiwuwar abin da ka iya faruwa idan aka sakankance aka raina wannan gargaɗi.

Iran ba ta samu ƙarfi ba ne ta hanyar kwaikwayon tsarin yamma. Ta gina ƙarfinta ne ta hanyar tsayuwar daka, jurewa takunkumai, da ƙirƙirar hanyar tasiri wadda ba ta dogara da sojoji kai-tsaye kaɗai ba. Wannan ya haifar da sabon yanayi a Gabas ta Tsakiya: yanayin da ba ƙasa guda ɗaya ke da cikakken iko ba, kuma inda duk wani motsi dole sai an yi shi cikin lissafi mai zurfi.

A nan ne mahangar falsafa ke bayyana. Iko, a ma’anarsa ta hikima, ba wai ikon kai hari ba ne kawai; ikon hana masu kai hari su kai hari ne. Idan ƙasa ta kai matakin da maƙiyanta ke fara matsar da kansu, ba domin sun sha kashi ba, sai domin sun gane hatsarin wuce-gona-da-irin da suke yi, to wannan ƙasa ta shiga wani sabon matsayin iko. Wannan shi ne abin da ke faruwa a yau.

Matakin Amurka da Birtaniya na kwashe wasu daga cikin ma’aikatansu ba lallai ne ya zama alamar rauni ba; amma alama ce ta gane canjin ma’auni. Yana nuna cewa Gabas ta Tsakiya ba za ta ƙara zama sansani mai sauƙin jibge sojojin yammacin duniya ba tare da sak**ako ba. Akwai ƙarfin da ke iya tasiri, ba da hayaniya ba, amma da tsari.

Masu s**ar Iran na iya cewa wannan iko yana haifar da rikici. Amma tambayar falsafa ita ce: shin rikici yana faruwa ne saboda akwai iko, ko saboda an ƙi karɓar sabon ma’aunin ikon? Tarihi ya nuna cewa mafi haɗarin lokuta su ne lokacin da tsohon iko ya ƙi amincewa da gaskiyar sabon iko.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kafa kanta a matsayin ƙasar da ba za a matsa mata lamba ba tare da farashi ba. Wannan matsayi, ko an yarda da shi ko ba a yarda ba, ya sanya ta zama ɓangare na lissafin duniya, ba wai batun yankin gabas kaɗai ba. Kuma a siyasar duniya, shiga lissafi ya fi shiga yaƙi muhimmanci.

Mujallar Hikima ba ta rubuta wannan maƙala domin ta yaba wa wata ƙasa kuma ta tsine wa wata ba. Ta rubuta ta ne domin ta nuna cewa duniya tana shiga sabon zamani na lissafin iko, zamanin da ba surutu ke yanke hukunci ba, sai hikimar lissafi, juriyar tsari, da ikon tsayawa kan matsayi.

A ƙarshe, tambayar ba ita ce shin ko Iran ta zama mai ƙarfin iko. Tambayar ita ce: shin duniya ta shirya karɓar sak**akon ƙarfinta? Domin duk lokacin da sabon gagarabadon iko ya bayyana, tsarin duniya dole ne ya sake fasali, ko an so ko ba a so ba.

© Mujallar Hikima
16/01/2026

"Tambaya ba ta rage imani; tana tsarkake shi ne. Imani kuma ba ya kashe hankali; yana tarbiyyantar da shi ne."~Mujallar ...
16/01/2026

"Tambaya ba ta rage imani; tana tsarkake shi ne. Imani kuma ba ya kashe hankali; yana tarbiyyantar da shi ne."

~Mujallar Hikima

Address

Rahamawa

824101

Opening Hours

Monday 09:00 - 22:00
Tuesday 09:00 - 22:00
Wednesday 09:00 - 22:00
Thursday 09:00 - 22:00
Friday 09:00 - 22:00
Saturday 09:00 - 22:00
Sunday 09:00 - 22:00

Telephone

+2348132252372

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujallar Hikima TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mujallar Hikima TV:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share