21/09/2025
RT. HONORABLE NASIR YAHAYA FULLY FUNDED SCHOLARSHIP.
Wannan shine tsarin tallafin karatu wanda mai Girma Speaker, Rt. Honorable Nasir Yahaya FISS, ya ɗauki nauyi. Wanda za’a biyawa ɗalibai 514 kudin registration, daga farko harsu kammala karatun su.
Wannan shine cikakken sunayen mutum 514 wanda Allah yasa za suci gajiyar wannan tsarin, bayan an gudanar da tantancewa. Wanda za suci moriyar tsarin sun kasance Marayu, da wanda iyayen su basa iya biya musu kuɗin registration.
Kwamitin wannan tallafin zasu fara biyan kuɗin makaranta daga gobe litinin 22/10/2025. Da misalin ƙarfe 9. Za a fara da makarantu kamar haka:
1- Yusuf Bala Usman College of Education Daura
2- Isah Kaita College of Education, Daura student center
3- Sarki Umar Faruq College (Almishkat)
Duk wanda Allah yasa yaga sunan shi cikin wannan tsarin, wanda ya kasance ɗaya daga cikin wannan makarantun da aka lissafa a sama, sai yayi ƙoƙari yazo da Original Admission letter ɗinsa, da kuma Registration number domin ya karɓi shaidar biyan kuɗin makarantar sa.
Domin ƙarin bayani, a tuntuɓi wannan lambobin. 08039275890, 07036749017, 08032204560, 08069770901, 08032303411, 08067203188 08135919000.
Dalhat Daura
SSA Digital Media
September 21st, 2025.