03/02/2024
Ba Laifi Bane Kayi Tunani Mai Kyau Da Lissafi A Rayuwa Da Qwaqwalwar Ka, Domin Dama Ai Manufar Da Tasa Allah Da Ya Halicci Mutum Ya Basa Tunani Da Hikima Ke Nan Domin Ya Gane Babancewa Tsakanin Qarya Da Gaskiya,
Amma Fa Hakan Bai Baka Dama Kana Ganin Cewa Kaima Kana Da Wata Dabara Ba Da Zata Cire Ka Ko Ta Saka A Matsala Ba Tare Da Cewa Kana Jingina Cewar Mafita Daga Allah Take Ba,
Domin Ubangiji Allah Subhanahu Wata'ala A Alqur'ani Cewa Yayi,
قل لن يصيبنا إلا ما كتب الله لنا هو مو لىنا وعلى الله فليتوكل المومنون.
Ma'ana Babu Fa Wata Musiba Ko Rahama Da Take Da Ikon Samun Mu Face Dama Allah Ya Rubuta Mana Ita.
Sannan A Wata Ayar Akan Halin Da Muke Ciki Allah Ya Riga Ya Fada.
ولنبلونكم بشىء من الخوف والجوع ونقص من الأموال والانفس والثمرت وبشر الصبرين.
Ma'ana Da Sannu Zamu Jarrabe Ku Da Wasu Abubuwa Kamar Tsoro Firgici (Rashin Tsaro) Da Yunwa,( Qarancin Abinci Ko Fari Ko Rashin Albarka Na Abinci) Da Qarancin Samun Kudi Koma Rashin Darajar Kudi, Da Qarancin Amfanunnuka Na Kayan Jin Dadi Na Ci , Amma Sai Allah Yace Masu Haquri Muna Yi Musu Bushara.
Masu Haqurin Nan Sune Wadanda Daga Cikin Dukkanin Wadannan Abubuwan Idan S**a Same Su Sai S**e- إنا لله وإنا إليه رجعون.
Zasu Fade Ta Ne Kuma Tare Da Bin Ma'anar Ta Ma'ana Sai Suyi Qoqarin Komawa Ga Allah Da Gyara Tsakanin Su Dashi Gasgatar Wasu Ayoyin Da Suke Cewa ما أصابك من حسنة فمن الله وما أصابك من سيئة فمن نفسك
أيضا
إن الله لا يغير ما بقوم حتى يغيروا ما بأنفسهم وإذا أراد الله بقوم سوءا فلا مرد له وما لهم من دونه من وال.
Wadannan Ayoyin Duka Idan Mun Kalli Ma'anonin Su Kamar Manuni Ne Ga Zamanin Da Muke Ciki Mu Fahimta Kuma Dole Mu Kasance Cikin
فردوه إلى الله والرسول إن كنتم تومنون با الله واليوم الآخر .
Saboda Haka Yan Uwa Wallahi Dole Mu Koma Ga Allah Mu Nemi Mafita Sannan Muyi Qoqarin Gyara Duk Inda Barnar Mu Take, Muyi Aiki Da Zahiri Sannan Mu Fifita Mafitar Mu Agurin Allah Sama Da Dabarun Da Duk Muke Ganin Sune Mafita, Domin Allah Yana Ganin Halin Da Muke Ciki Kuma Yana Da Ikon Cire Mu Sanda Yaso.
Wannaan