Ishaq T. Auta

Ishaq T. Auta Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ishaq T. Auta, Digital creator, Dangau Sandamu, Daura.

12/10/2024
Happy Independence Day
01/10/2024

Happy Independence Day

13/03/2024

Game Da Azumin Awa 3 A Ƙauyen
WEKAN na Ƙasar Oman
Ba wannan ne karo na farko ba, kusan duk watan Azumin Ramadan
tun daga shekarar 2015 sai an yaɗa labarin ƙauyen WEKAN na Ƙasar
Oman a matsayin garin da ake azumin tsawon awanni 3 kacal daga
hudowar rana zuwa faduwar ta. Har wasu ma cikin masu yaɗa
labarin ke marmarin ina ma da ko za su samu hanyar tafiya can don
samun sauƙin Azumin musamman a lokutan da ake matsanancin
zafi a yankin Sahara.
MENE NE GASKIYAR LAMARIN?
Wekan, wani ɗan tsibirin ƙauye ne da ke da tazarar nisan kilomita 150
daga babban birnin Ƙasar Oman wato Muscat ta ɓangaren yamma.
Ƙauye ne da mafi sauƙin abun hawan da za ka yi amfani da shi zuwa
cikin sa shine Jakuna da Dawakai da kuma manyan motoci masu iya
keta duwatsu da kwazazzabai (a shekarar 2013 kenan) amma a
yanzu an samar da hanyar mota mai kyau har cikin ƙauyen a dalilin
tambarin da sunan garin ya yi a duniya dalilin jita-jitar da ake ta
yaɗawa na azumin awanni 3.
Haka nan dai, ƙauye ne wanda babban madogarar kuɗin shigar
mutanen cikin sa shi ne sayar da kayan marmari sakamakon albarkar
ƴaƴan itatuwa da su ke da shi nau’uka daban-daban. Sai kuma a
baya bayan nan da ake samun masu zuwa yawon buɗe da
tabbatarwa da wancan jita-jitar azumin awa uku ɗin.
Sannan wani abu da ya kamata mutane su sani a nan shi ne, a kaf
faɗin ƙasar Oman, ƙauyen WEKAN ne kaɗai garin da ke tsakiyar
manyan tsaunukan da in ban da Ƙasar Saudiyya, a kaf gabas ta
tsakiya, babu in da ya kai yankin da ƙauyen ya ke dogayen tsaunuka.
Wannan ya sa, idan rana ta hudo daga gabas da sanyin safiya, sai
kimanin wajen ƙarfe 11 na safen sannan mutanen garin ke ganin
ranar. Saboda tare ta da waɗannan tsaunukan ke yi.
Kuma duk in da ƙarfe 2 zuwa 2:30pm ta yi, daga nan ranar ta ke ɓace
musu da gani sakamakon kwantawa da ta ke yi zuwa ɓangaren
yamma wanda nan ma dai tsaunin ne ke tare ta ba wai don ta faɗi ba
ne a ɗaukacin ƙasar Oman ɗin ba.
Kenan mutanen ƙauyen Wekan, na ganin rana ƙuru-ƙuru ne na iya
tsawon awanni uku zuwa da rabi.

Address

Dangau Sandamu
Daura

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ishaq T. Auta posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share