Al-ihsan Islamic Da'awa and Charity Foundation

Al-ihsan Islamic Da'awa and Charity Foundation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al-ihsan Islamic Da'awa and Charity Foundation, TV Channel, Address: No. 27th, Bunturawa Road Opposite Keystone Bank Shaiskawa Quarters Daura, Daura.

12/08/2026

Hadisinmu Na Yau Laraba 28 Safar 1448 (12-08-2026)

Manzon Allah SAW ya ce; Duk wanda ya cutar da wani mutum a kan mutuncinsa ko a wani abu, to ya roƙe shi ya gafarta masa kafin ranar Al-Qiyama, ranar da babu sauran dukiya (da za a iya maye gurbin munanan ayyuka da ita), amma idan mutum yana da kyawawan ayyuka, waɗannan kyawawan ayyukan za a ɗauko na sa gwargwadon cutarwar da ya yi, idan kuma bai da kyawawan ayyuka, zunuban wanda ya cutar za a ɗauko a ɗora masa.

Narrated Abu Huraira RA:

Allah's Messenger PBUH said, "Whoever has oppressed another person concerning his reputation or anything else, he should beg him to forgive him before the Day of Resurrection when there will be no money (to compensate for wrong deeds), but if he has good deeds, those good deeds will be taken from him according to his oppression which he has done, and if he has no good deeds, the sins of the oppressed person will be loaded on him."

Sahih Al-Bukhari No. 2449

11/08/2026

Hadisinmu Na Yau Talata 27 Safar 1448 (11-08-2026)

Nana A'isha ta ce: Wata rana Manzon Allah SAW ya shigo, a lokacin wata mata na zaune a kusa da ni. Sai ya ce, Wacece wannan? Sai na ce, wance ce (ta yi bayanin wacece baƙuwar), sai na faɗa masa yanda take tsanantawa wajan sallah. Sai ya ce cikin rashin jin daɗi, Ki yi aiyukan alkhairi gwargwadon iyawarki, domin Allah ba Ya gajiya (wajan bada sakamako) amma ke za ki gaji, kuma mafi alkhairin aiki a wajan Allah shi ne wanda aka dawwama ana yi.

Narrated by Aisha RA:

Once the Prophet PBUH came while a woman was sitting with me. He said, "Who is she?" I replied, "She is so and so," and told him about her (excessive) praying. He said disapprovingly, "Do (good) deeds which is within your capacity (without being overtaxed) as Allah does not get tired (of giving rewards) but (surely) you will get tired and the best deed (act of Worship) in the sight of Allah is that which is done regularly."

Sahih Al-Bukhari No.

10/08/2026

Hadisinmu Na Yau Litinin 26 Safar 1448 (10-08-2026)

Manzon Allah SAW ya ce; Shin ba na sanar da ku abin da ya fi falala fiye da yin nafilar azumi, sallah da sadaka ba?
Sahabbai su ka ce; Eh ya RasululLah. Annabi SAW ya ce; Sasanci a tsakanin mutane. Domin tabbas ɓata alaƙa tsakanin mutane mayanka ce (wato tana yanke addini).

Abu Darda'i RA reported:

The Messenger of Allah PBUH, said; “Shall I not tell you of what is better in degree than extra fasting, prayer, and charity?” They said, “Of course!” The Prophet PBUH said, “Reconciliation between people. Verily, spoiling relations between people is the razor.”

Sunan Abi Dawud No. 4919
Jami' At-Tirmidhi No. 2509
Sahih Ibn Hibban No. 5092
Sahih Al-Targhib wa Al-Tarhib No. 2814.

09/08/2026

Hadisinmu Na Yau Lahadi 25 Safar (09-08-2026)

Wani Balaraben ƙauye mai gashi a cukuikuye ya zo wajen Manzon Allah SAW ya ce:

Ya Manzon Allah sanar da ni abin da Allah Ya wajabta a kaina game da sallah.

Sai Manzon Allah ya amsa : Ka yi salloli cikakku sau biyar a wuni da dare, sai idan ka so ka yi Nafila.

Mutumin ya ƙara tambaya; Sanar da ni abin da Allah Ya wajabta ma ni game da azumi.

Sai Annabi ya amsa: Ka yi azumin watan Ramadan gaba ɗaya, sai idan kana so ka ƙara a matsayin Nafila.

Mutumin ya ƙara tambaya; Fada mani adadin Zakkar da aka ɗora ma ni.

Kuma sai Manzon Allah ya sanar da shi duka dokokin musulunci.

Sai mutumin ya ce; Na rantse da (Allah) wanda Ya darajta ka, ba zan yi wata Nafila ba, kuma ba zan rage daga abin da Allah Ya wajabta mani ba.

Manzon Allah ya ce: idan gaskiya yake faɗi zai yi nasara (ko kuma za a shigar da shi Aljannah).

Narrated by Talha bin Ubaidullah RA:

A Bedouin with unkempt hair came to Allah's Messenger PBUH and said;

"O Allah's Messenger! Inform me what Allah has made compulsory for me as regards the prayers."

He replied: "You have to offer perfectly the five compulsory prayers in a day and night (24 hours), unless you want to pray Nawafil."

The Bedouin further asked, "Inform me what Allah has made compulsory for me as regards fasting."

He replied, "You have to fast during the whole month of Ramadan, unless you want to fast more as Nawafil."

The Bedouin further asked, "Tell me how much Zakat Allah has enjoined on me."

Thus, Allah's Messenger PBUH informed him about all the rules (i.e. fundamentals) of Islam.

The Bedouin then said, "By Him Who has honored you, I will neither perform any Nawafil nor will I decrease what Allah has enjoined on me.

Allah's Messenger PBUH said, "If he is saying the truth, he will succeed (or he will be granted Paradise)."

Sahih Al-Bukhari No. 1891
Sahih Al-Bukhari No. 46
Sunan Abi Dawud No. 391.

08/08/2026
08/08/2026

TAFSIRIN ALQUR'ANI MAI GIRMA KARATU A CIKIN SURATUL FUSSILAT DAGA MASALLACIN KARAMA DAURA OPPOSITE FGC
08/08/2026 24 SAFAR 1448AH TARE DA IMAM HABIB MAGAJI KARKARKU, DA Alaramma MALAM SANI MAGAJI.

08/08/2026

Hadisinmu Na Yau Asabar 24 Safar 1448 (08-08-2026)

Manzon Allah SAW yana karanta wannan addu'ar a duk lokacin da ya gama cin abinci:
"AlhamdulilLah kathiran ɗaiyiban mubarakan fihi ghaira makfiy wala muwada' wala mustaghna'anhu Rabbuna."

Narrated Abu Umama RA:

Whenever the Prophet PBUH finished his meals (or when his dining sheet was taken away), he used to say. "Praise be to Allah Who has satisfied our needs and quenched our thirst. Your favor cannot by compensated or denied." Once he said, praise be to You, O our Lord! Your favor cannot be compensated, nor can be left, nor can be dispensed with, O our Lord!"

Sahih Al-Bukhari No. 5459

06/08/2026

KARATUN LITATTAFAI AL'AGSANIN NADIYYA SHARHUL KULASATUL BAHIYYA FIY TARTIBI AHDAASUS SIRATUN NABAWIYYA DARASI NA 20
الأغصان الأندية شرح الخلاصة البهية في ترتيب أحداث السيرة النبوية
MAI GABATARWA IMAM MALAM HASSAN YUSUF DAURA MASALLACIN KARAMA DAURA OPPOSITE FGC DAURA 06/08/2026 22 SAFAR 1448AH

06/08/2026

Hadisinmu Na Yau Alhamis 22 Safar 1447 (06 August 2026)

Abu Qatada RA ya ce:
Na ji Manzon Allah SAW yana cewa; Mafarki kyakkyawa daga Allah ne, Mafarki mummuna kuma daga Shaiɗan ne. Idan ɗayanku ya yi mafarkin abin da ba ya so, ya yi tofi sau uku a hannunsa na hagu, Ya nemi tsarin Allah daga cutarwar mafarkin, idan ya yi haka ba zai cutar da shi ba.

Narrated Abu Qatada RA:

I heard the Prophet PBUH saying, "A good dream is from Allah, and a bad dream is from Satan. So if anyone of you sees (in a dream) something he dislikes, when he gets up he should blow thrice (on his left side) and seek refuge with Allah from its evil for then it will not harm him."

Sahih Al-Bukhari.No. 5747

Address

Address: No. 27th, Bunturawa Road Opposite Keystone Bank Shaiskawa Quarters Daura
Daura
824101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-ihsan Islamic Da'awa and Charity Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category