ARISH MEDIA

ARISH MEDIA Always ready capture the best events, ceremonies and adverts for you ���

Contact Us: 07047114799

🎉 ARISH MEDIA NA TAYA SHUGABANTA MURNAR RANAR HAIHUWA 🎉A yau, iyalan Arish Media suna farin cikin taya shugaban ta Hon A...
09/06/2026

🎉 ARISH MEDIA NA TAYA SHUGABANTA MURNAR RANAR HAIHUWA 🎉

A yau, iyalan Arish Media suna farin cikin taya shugaban ta Hon Auwal Rabiu Isah MKY, murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Muna godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ƙara maka shekara cikin koshin lafiya, zaman lafiya da albarka. Muna yaba wa jajircewarka, hangen nesanka da kuma gudummawar da kake bayarwa wajen yaɗa sahihan labarai da inganta al’umma

A wannan rana mai albarka, muna roƙon Allah Ya ƙara maka lafiya, hikima, nasara da ɗaukaka. Ya sa rayuwarka ta kasance cike da alkhairi, Ya albarkaci iyalanka da dukkan ayyukanka na alheri

Barka da zagayowar ranar haihuwa Hon Auwal Rabiu Isah MKY
Allah Ya ƙara shekaru masu albarka cikin biyayya gare Shi🤲🏻🤲🏻🎂🎂🤲🏻🤲🏻

Daga: Arish Media 🖋️📺📰

DA DUMI-DUMI: Pantami Ya Janye Daga Zaben Fidda Gwani Na Takarar Gwamna A Jam’iyyar APC, Saboda Take Hakkin Tsarin Zabe ...
19/05/2026

DA DUMI-DUMI: Pantami Ya Janye Daga Zaben Fidda Gwani Na Takarar Gwamna A Jam’iyyar APC, Saboda Take Hakkin Tsarin Zabe Da Rashin Bin Doka
....Nan bada dadewa ba zamu sanar da matsayarmu ga magoya bayanmu.
...Kudirin tafiyar Pantamiyya na tabbatar da kyakkyawan shugabanci a jihar Gombe da Najeriya yana nan daram, haka kuma matsayinta na yaƙi da rashin adalci ta hanyar bin doka ba zai girgiza ba.

Professor Isa Ali Ibrahim Professor Isa Ali Pantami CON, PhD (Prof/Malam Pantami), ya janye daga takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC domin nuna rashin amincewarsa da take haƙƙoƙin Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma gazawar jam’iyyar wajen samar da hanyoyin sadarwa da bayanan da suke da muhimmanci domin gudanar da sahihin zaɓe.

Lokacin da Prof. Pantami ya amsa ƙiran shugabanni, matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki da s**a nemi ya tsaya takarar gwamnan Jihar Gombe, ya nuna cikakkiyar biyayya da aminci ga APC ta hanyar bin dukkan ƙa’idoji, cika sharuɗɗa da bin hanyoyin da aka shimfiɗa. Shi ne kaɗai ɗan takarar gwamna na APC da ya aika wakili zuwa taron yarjejeniyar zaman lafiya da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Gombe ta shirya a ranar 14 ga Mayu, 2026. Wakilinsa ne kaɗai ya sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiyar a yayin taron.

Duk da irin wannan biyayya da girmamawa ga jam’iyya, an ci gaba da hana shi samun muhimman bayanai. Wasiƙun da lauyoyinsa s**a aika zuwa sassa daban-daban na jam’iyyar suna neman bayanai tare da bayyana damuwa kan yadda za a gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna ba su samu amsa ba ko da tabbacin karɓa ba. Har yanzu ba a magance waɗannan matsaloli ba.

A tsarin dimokuraɗiyya, doka ce ya kamata ta jagoranci komai. Rashin bin Dokar Zaɓe ta 2026 da ƙa’idojin jam’iyya ya sa wannan tsari ya zama maras inganci kuma abin tambaya. Al’ummar Jihar Gombe sun ga abin da ya faru a zaɓukan fidda gwani na Majalisar Tarayya da aka gudanar a ranakun 16 da 18 ga Mayu, 2026. Ƙarfin Prof. Pantami ya dogara ne daga ɗimbin goyon bayan jama’a musamman matasa da mata. Sai dai abin takaici, a zaɓukan da aka gudanar kwanan nan, an ware mambobin jam’iyya na matakin ƙasa (tushe) daga tsarin.

Bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki da kuma nazari kan abubuwan da suke faruwa a Jihar Gombe, Prof. Pantami ya ɗauki matakin janyewa daga zaɓen fidda gwani na gwamna da aka shirya gudanarwa ranar 21 ga Mayu, 2026, a matsayin zanga-zangar lumana. Zanga-zangar lumana wani ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya.

Wannan mataki ya samo asali ne daga yadda aka yi watsi da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 da kuma gazawar shugabancin jam’iyya wajen aiwatar da tsarin da zai tabbatar da sahihin zaɓen fidda gwani. A lokacin zaɓukan fidda gwani na Majalisar Tarayya, babu sahihin zaɓe da aka gudanar a jihar. Bisa ga bayanan da wasu ‘yan takara s**a bayar, ba a sanar da wuraren gudanar da zaɓe, hanyoyin gudanarwa ko tsarin tantance wakilai da masu sa ido ba, amma daga baya aka bayyana sakamako.

Duk da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada muhimmancin gudanar da sahihin zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci, abin takaici umarninsa ba su samu aiwatarwa ba. Prof. Pantami ya nemi bayanai kan lokaci da wurin tantance wakilai da masu sa ido, hanyoyin tantancewa, kaɗa ƙuri’a da tattara sakamako, da kuma wuraren tattara sakamako. Waɗannan bayanai ya kamata a bai wa dukkan ‘yan takara ba tare da sun nema ba. Zuwa wannan lokaci, babu abin da aka bayar.

Prof. Pantami yana miƙa godiya ta musamman ga matasan da s**a haɗa kuɗi domin sayen fom ɗin nuna sha’awa da tsayawa takara a gare shi. Gudummawar da aka bayar ta fara daga naira dubu biyar zuwa miliyan huɗu, kuma an fitar da rasit tare da wallafa su a kafafen sadarwa. Haka kuma yana gode wa magoya bayansa musamman matasa da mata, da masu gudanar da aiki a rumfunan zaɓe, gundumomi, ƙananan hukumomi da faɗin Jihar Gombe, da ƙungiyar yaɗa labarai, dattawa da Kwamitin Gudanar da Yaƙin Neman Zaɓensa saboda jajircewa da fahimta da s**a nuna. Ya buƙaci dukkan magoya baya su kasance masu natsuwa da bin doka domin kare zaman lafiya da tsaro a jihar. Dimokuraɗiyya tana tafiya ne da doka, zaman lafiya da tsaro.

Tafiyar Pantamiyya za ta sanar da mabiyanta, magoya baya, masu fatan alheri da ɗaliban Prof. Pantami a Jihar Gombe da faɗin Najeriya matakan da za ta ɗauka nan gaba a lokaci mai zuwa. Ƙudirin tafiyar na tabbatar da kyakkyawan shugabanci a Jihar Gombe da Najeriya yana nan daram, haka kuma matsayinta na yaƙi da rashin adalci ta hanyar bin doka ba zai girgiza ba. Ana ƙira ga dukkan mabiyan Malam Pantami da magoya bayansa su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai domin tunkarar matakai masu zuwa a harkar siyasa.

Allah Ya albarkaci Jihar Gombe, Tafiyar Pantamiyya da Tarayyar Najeriya.

Barrista Ibrahim M. Attahir
(A madadin Tafiyar Pantamiyya)
19 ga Mayu, 2026

YANZU-YANZU : Kotu ta bayar da belin Nasir El-Rufai kan kuɗi Naira miliyan 100.Mai shari’a Joyce Abdulmalik, a hukuncint...
18/05/2026

YANZU-YANZU : Kotu ta bayar da belin Nasir El-Rufai kan kuɗi Naira miliyan 100.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik, a hukuncinta, ta bayyana cewa wanda zai tsaya masa a matsayin wanda zai karbi belinsa dole ne ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro da ke Abuja sannan kuma ya ajiye asalin takaddar mallakar fili a rajistar kotu.

Me za ku ce?

SAKON TAYA MURNAA madadin Shugabanci da ma’aikatan Arish Media, muna taya HON. AUWAL RABIU ISAH MKY murna bisa samun wan...
05/05/2026

SAKON TAYA MURNA

A madadin Shugabanci da ma’aikatan Arish Media, muna taya HON. AUWAL RABIU ISAH MKY murna bisa samun wannan lambar yabo.

Wannan karramawa na nuna jajircewarsa da gudummawarsa wajen cigaban matasa da al’umma.

Muna masa fatan alheri

– Shugaban Kamfanin Arish Media

⸻SANARWAR AMINCEWA DA TSAYAWA TAKARAR KUJARAR MAJALISAR TARAIYA SANDAMU/DAURA/MAI ADUA DAGA Hon Auwal Rabiu IsahAssalamu...
17/04/2026



SANARWAR AMINCEWA DA TSAYAWA TAKARAR
KUJARAR MAJALISAR TARAIYA SANDAMU/DAURA/MAI ADUA DAGA Hon Auwal Rabiu Isah

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh,

Alhamdulillahi, muna godewa Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba mu rai, lafiya, da damar haɗuwa a wannan lokaci mai muhimmanci.

Ina miƙa godiya ta musamman ga al’ummar Sandamu, Daura da Mai’Adua bisa irin goyon baya, amincewa da ƙaunar da kuka nuna min. Wannan amincewa taku ce ta bani ƙwarin gwiwa da ƙarfafa ni na ɗauki wannan muhimmin mataki.

A yau, cikin tawali’u da cikakken nauyin da ke kaina, ina tsaye a gabanku domin na amince da kiran jama’a, tare da bayyana aniyata ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Tarayya a zaɓen 2027, Insha Allah.

Manufata ta haɗa da:
• Inganta rayuwar al’umma
• Samar da ayyukan yi ga matasa
• Tallafawa ilimi da cigaban yara
• Kawo ci gaba mai ɗorewa a yankinmu
• Tabbatar da gaskiya da riƙon amana a shugabanci

Ina tabbatar muku cewa zan kasance wakili mai sauraron jama’a, mai aiki tukuru, kuma mai kare muradunku a Majalisar Tarayya.

Ina roƙon ku da ku ci gaba da bani goyon baya, addu’a da haɗin kai domin cimma wannan buri.

Nagode ƙwarai.



HON. AUWAL RABIU ISAH (MKY)
Mai neman takarar Majalisar Tarayya
Sandamu / Daura / Mai’Adua
Jihar Katsina

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Uwargidan Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Hajia Maijidda Abdulkad...
14/04/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Uwargidan Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Hajia Maijidda Abdulkadir Mamman Nasir Ta Rasu Yau Talata, Bayan Gajeruwar Rashin Lafiya

Allah Ya Jikanta Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un!Allah tayiwa  Alhaji Kabir Salisu DAN MAJEN DAURA rasuwa yauZa'ayi Jana'izar sa  Insh...
14/04/2026

Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un!

Allah tayiwa Alhaji Kabir Salisu DAN MAJEN DAURA rasuwa yau

Za'ayi Jana'izar sa Insha Allah da karfe biyar na yamma 5.00pm a gidansa dake kusa da Rijiyar Kusugu.

Allah gafarta masa Yasa Aljannar Firdausice masaukinsa, ameen!
14/04/2026

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’unA madadin kamfanin ARISH MEDIA da dukkan ma’aikatansa baki ɗaya, muna miƙa sakon ta’a...
25/03/2026

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un

A madadin kamfanin ARISH MEDIA da dukkan ma’aikatansa baki ɗaya, muna miƙa sakon ta’aziyya mai cike da alhini da jimami zuwa ga Mai Girma Sarkin Karafan Daura, Alhaji Muzambilu Daura, bisa rasuwar mahaifiyarsa jiya.

Hakika mutuwa gaskiya ce, kuma kowa zai ɗanɗana ta. Wannan babban rashi ne ga iyali, ‘yan uwa da al’umma baki ɗaya. Muna roƙon Allah Ya ba ku haƙuri da juriya wajen jure wannan rashin, Ya kuma ƙarfafa zukatanku.

Muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalai, ‘yan uwa da dukkan masoya. Muna addu’ar Allah (SWT) Ya jiƙan marigayiyar, Ya gafarta mata zunubanta, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarta.

Allah Ya ba ku ƙarfin zuciya da juriyar wannan babban rashi. Amin.

Daga:
Hon. Auwal Rabiu Isah Bulaman Daura
Shugaban Kamfanin ARISH MEDIA
A madadin dukkan ma’aikatan ARISH MEDIA

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Soke Hawan Sallah, Ta Tabbatar Da Sarki Sunusi A Matsayin Wanda Zai Jagoranci Sallar IdiG...
18/03/2026

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kano Ta Soke Hawan Sallah, Ta Tabbatar Da Sarki Sunusi A Matsayin Wanda Zai Jagoranci Sallar Idi

Gwamnatin Jihar Kano ta soke Hawan Sallah da aka saba gudanarwa a bana, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.

Sai dai duk da hakan, gwamnatin ta tabbatar da cewa Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci Sallar Idi kamar yadda aka saba. Haka kuma, an amince da gudanar da Hawan Nasarawa amma a sabon tsari, ba tare da hawa doki ba, sai dai ta amfani da mota.

Me za ku ce?

DA DUMI-DUMI: Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare, zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC. Me za ku ce?
09/03/2026

DA DUMI-DUMI: Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare, zai fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Me za ku ce?

Address

Sabon Gari
Daura

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ARISH MEDIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share