13/04/2025
Da dumi'dumi: Shugaba Tinubu Ya fara Yunkurin Sauke Ganduje daga shugabancin APC domin maye gurbin sa da Tanko Al-makura.
Jaridar Vanguard ta ruwaito tana mai cewa Yayin da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na shekarar 2027 ke kara ta’azzara, rahotanni da ke fitowa sun nuna cewa, bangaren shugaban kasa Bola Tinubu na yunkurin hana manyan ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sauya sheka zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), musamman na jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC).
Wata sanarwa da aka fallasa ta bayyana cewa, shugaba Tinubu na tunanin tsara tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura, na hannun daman tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin shawo kan kungiyar CPC ta ci gaba da zama a APC.
Rahotanni sun bayyana cewa ana yi wa Al-Makura tayin kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa domin ya gamsar da Buhari ya sa baki tare da hada kan magoya bayan sa.
Majiyoyi sun bayyana cewa Al-Makura ya shirya ganawa da manema labarai a ranar Litinin, inda ake sa ran zai bayyana goyon bayan da ake zargin Buhari na ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyar APC.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa a cikin jam’iyyar mai mulki, yayin da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa da s**a hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, da kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Achike Udenwa, ke neman wasu wasu tsare-tsare na siyasa kafin shekarar 2027, saboda rashin gamsuwa da shugabancin Tinubu.
Takardar ta kara bankado yadda ake samun tabarbarewar cikin gida a cikin jam’iyyar APC tare da sanya ayar tambaya kan hadin kan jam’iyyar da kuma makomarta gabanin zabukan na gaba.