24/09/2025
Sakon Goyon Baya ga Chief Iliya Ezekiel Dasen – Dan Takarar Da Talakawa Ke Bukata a 2027
Mu mutanen Donga, Takum, Ussa da Yangtu Special Development Area mun san gaskiya – babu wani dan siyasa da ya nuna gaskiya, kishin kasa da tausayin talakawa kamar Chief Iliya Ezekiel Dasen. Kodayake bai taba rike wani matsayi na zabe ba, ayyukansa sun wuce na wadanda ke kan madafun iko.
Chief Dasen ya sadaukar da kansa wajen taimakon al’umma, yana tsayawa tsayin daka wajen ganin cewa rayuwar jama’a ta inganta – ba tare da wani son zuciya ba. Ya zama amintaccen uba, aboki, da mai ba da fata ga dubban talakawa da ke fatan ganin rayuwa mai kyau.
Saboda haka, muna kira da karfi da yaji, muna rokon Chief Iliya Ezekiel Dasen da ya tsaya takara a matsayin mamba na House of Representatives a 2027 domin wakiltar mu da adalci, nagarta da cancanta.
Talakawa sun farka. Lokacin gaskiya ya yi. Lokacin Dasen ya yi.