01/11/2025
1/11/2025
LABARUN KARSHEN MAKO A DUKKU, GOMBE
A cikin takaitattun labarun mu na karshen wannan mako, za ku ji cewa:
1- Mai girma gwamnan jihar Gombe Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya CON (Dan Majen Gombe) ya turo komitin kula da hulda tsakanin Manoma da Makiyaya zuwa fadar mai martaba Sarkin Dukku. Domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin su.
2- Komishinan Gona, da albarkatun kasa na jihar Gombe Dr. Barnabas Malle ya yi kira ga Manoma da Makiyaya dasu zauna da juna lafiya. Tare da sasanta tsakanin su ba tare da zuwa Kotu ba.
3- Mai martaba Sarkin Dukku HRH Alh. Haruna Rashid || CON ya shawarci Manoma da Makiyaya dasu zama masu aiki da dokoki da ka'idojin gwamnati a guraren Kiwo da Noma.
4- Mai martaba Sarkin Dukku HRH Alh. Haruna Rashid || CON ya karrama Zakarun musabakar Al-Qur'ani na bana 2025 a matakin karamar hukumar Dukku a fadar sa Mai albarka.
5- Wakilin Dukku/Nafada a majalisar tarayyar Najeriya Hon. Abdullahi El-Rasheed ya yi gyara, tare da sabunta ajujuwa, da ofishin Malamai a makarantar Duggiri dake gundumar Malala.
6- Shugaban karamar hukumar Dukku Hon. Adamu Mohammed Waziri (Wazirin Dukku) ya gyara rumbun wutar Lantarki (Transformer) dake bakin sakatariyar karamar hukumar Dukku. Bayan ya shafe shekara 8 baya aiki.
7- Shugaban karamar hukumar Dukku Hon. Adamu Mohammed Waziri (Wazirin Dukku) ya kaddamar da biyan kudaden filaye, da gonaken da aka dauka domin gina filin wasanni (Stadium) irin na zamani a Dukku.
8- Hon. Aishatu Jibir Dukku (Gimbiyar Dukku) ta fidda sanarwar neman masu bukatar karatu a makarantar Legal Nafada, domin ta saya musu Form, sannan tayi musu rijista kyauta.
9- Hon. Jamilu Ahmed Shabewa ya dauki nauyin abincin gwarazan musabakar Al-Qur'ani, wadan da zasu wakilci Dukku a Nafada domin shiga musabaka a matakin jihar Gombe.
10- Al'ummar gundumar Lafiya/Tale sun mika bukatar neman karamar hukumar Dukku ta bude musu kasuwa a garin Lafiya, domin bunkasa tattalin kasar su
11- Al'ummar cikin garin Dukku sun fara kururuwar kukan rashin ruwan Sha a cikin garin Dukku.
12- Zirga-zirgar masu diban ruwa a cikin garin Dukku ya kank**a hajaran majaran a tafkunan Kogin Dole, Tafkin Shabewa, da Mbela Bamba.
13- Mal. Kasimu Gimba ya yi kira ga mai girma gwamnan jihar Gombe, da shugaban karamar hukumar Dukku dasu tausaya wa marayu, da masu kananan karfi wajen biyan kudaden filaye, da gonaken da aka dauka domin gina filin wasanni (Stadium) a Dukku.
14- Matasa masu fafutuka a zaurukan sada zumunta (Internet) domin neman a gyara hanyar Gombe, Dukku, zuwa Darazo sun fidda sabon salon sanya hotunansu cikin hatimi. Domin bayyana ma Duniya damuwar su na neman a gyara musu hanya.
15- Rashin babban Likita a Asibitotin gwamnati a karamar hukumar Dukku ya jefa fargabar tabarbarewar kiwon lafiya a zukatan al'ummar kasar Dukku.
16- Anyi gudun famfalaki a tsakin barawon Babur da masu kolala a General Hospital Dukku. Sai dai masu kolala basu yi nasarar k**a Barawon ba!
17- Barawo ya yi awun gaba da Babur din limamin masu salla a rumfar kasuwa, a dai-dai lokacin da suke sallar Isha'i a cikin kasuwar Dukku.
18- Masu kiwon tsuntsaye suna ci gaba da kukan yadda karnuka suke cinye musu Kaji, saffan Agwagi, da 'ya'yan Tolo-tolo a unguwar Tudun Magaji a cikin garin Dukku.
19- Matan da Wazirin Dukku ya maida su kan turbar Karatu a karkashin shirin AGILE sun fara kwarewa a fannin koyon Dinki da Sakan kayan sanyi na yara.
20- Magoya bayan jam'iyyar PDP sun yi kukan zuci bisa sabon salon Wazirin Dukku na yin zama da Mata magoya bayan su, tare da yi musu ihsani.
21- Manyan Mata jiga-jiga jam'iyyar PDP sunyi gangamin tabbatar da goyon bayan su ga Hon. Bala Kelly a gidan Haj. Adda Iya a unguwar Tudun Magaji a cikin garin Dukku.
22- An bayyana dacewar daukan matakin ladabtarwa akan Manomin daya dauki Mata 22 a Dukku, ya kaisu aiki a gonarsa dake kasar Zange (Feshare) ya barosu. Wasun su a kafa s**a dawo, yayin da wasu s**a sayar da woyoyin su a hanya domin samun kudin Babur din dawowa.
Rahoto
Umar Babagoro Dukku
Shetiman Nakuja
Auwal Seaman
Umar Mohammed Dukku
Bibiya da gyara tuntuben alkalami
Comr Huzaifa Ayuba