Ar-raihaan Multimedia

Ar-raihaan Multimedia Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ar-raihaan Multimedia, Digital creator, T/wada, Dukku.

🕌إِنَّ الَّذِينَ يَتْلُونَ كِتَابَ اللَّهِ وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَأَنفَقُوا مِمَّا رَزَقْنَاهُمْ سِرًّا وَعَلَانِيَةً يَرْجُونَ تِجَارَةً لَّن تَبُورَ🕌

✨لِيُوَفِّيَهُمْ أُجُورَهُمْ وَيَزِيدَهُم مِّن فَضْلِهِ ۚ إِنَّهُ غَفُورٌ شَكُورٌ✨

Idan kanaso Kasamu sauki cikin Al'amuranka To ka yawaita ISTIGFARIKa lazimci istigfari,domin shi ne mabuɗin samun sauƙi,...
27/08/2026

Idan kanaso Kasamu sauki cikin Al'amuranka To ka yawaita ISTIGFARI

Ka lazimci istigfari,domin shi ne mabuɗin samun sauƙi, da kawar da damuwa, da jawo arziki, da gafarar zunubai. Ka dage da faɗin
__Astaghfirullah__
ko Astaghfirullāhal-Azīm wa atūbu ilaih
cikin yaƙini da halartacciyar zuciya. Haka kuma za ka iya amfani da wasu lafuzza kamar “Sayyidul Istigfār”. Istigfari yana sauya ƙunci zuwa mafita, kuma yana kawo arziki daga inda mutum bai zata ba.

Ar-raihaan Multimedia

26/08/2026

اللهم إنى أعوذ بك من الحَوْرِ بعدَ الكَوْرِ

kada ka yi wasa da ita, ka riƙa yi sosaii
Allah raba mu da fitina

Ar-raihaan Multimedia
26/08/2026

Ar-raihaan Multimedia

23/08/2026

Yan uwa ɗalibai kar mu shagala daga barin asalin manufar karanta Alqur'ani.

Babban manufar karantar Alqur'ani, shine tadabburin ayoyin. 'كِتَابٌ أَنزَلْنَاهُ إِلَيْكَ مُبَارَكٌ لِّيَدَّبَّرُوا آيَاتِهِ وَلِيَتَذَكَّرَ أُولُو الْأَلْبَابِ'

An karanta ayoyin gargaɗi, albishir, azaba, rahama da sauran su amma babu bambanci a reaction ɗin mu. Anya babu buƙatan mu gyara.

Musamman a irin munasabobin taro na karanta Alqur'ani, da mai karatu da mai karantawa sai sun yi takatsantsan. Wasu lokuta mutum zai zo yana karanta Alqur'ani da zuciya mai kyau, yayin da karatun yayi daɗi kunnen masu sauraro, sai su yi wasu kabbarori ko kalamai na rashin nutsuwa wanda zasu iya tasiri a zuciyan mai karatu ya taɓa masa niyyar sa. Wani lokaci kuma, shi mai karatun musamman zai zo yayi salon karatun da yana buƙatan irin waɗannan abubuwa. Da za'a zo ba'a ƙira yayi karatu ba sai yaji babu daɗi, don bai isar da abunda yake son isarwa ba na nuna bajinta da ƙwarewa. A irin haka ma har ya ɗauko karatu da riwayar da bai da sani a kan ta.

Aikin ibada da gurɓataccen niyya gara rashin sa. Hakan ba ya kore kyautata sautin karanta Alqur'ani. Amma akwai abunda kana kwata kwata ba ya cikin kyautata karanta Alqur'ani, sai dai ma ya shiga cikin wasa da Alqur'ani da rashin mutunta shi. Kar dai neman yardan mutane da yabo daga gare su ya zamo shine gaaya.

Allah yasa mu dace, ya kare mu daga zamiya a dukkan ayyukan mu, Amin.


23/08/2026

Ga Dalilin Dake sa kaga Mutum Mai ilimi Amma da Girman Kai 👇👇👇

1. Ilimi ba tare da tarbiyya ba
Idan ilimi bai zo tare da tarbiyyar zuciya ba, yana iya zama hujja a kansa. Mutum yana ganin ya fi kowa sani, amma bai koyi yadda zai saukar da kansa ba.

2. Sha’awar yabon mutane
Wasu suna neman a riƙa yaba musu saboda iliminsu. Idan s**a saba da yabon jama’a, sai zuciya ta fara ɗaga—har ya zama suna jin sun fi sauran.

3. Mantawa da asalin ilimi
Mutum ya manta cewa ilimi daga Allah ne. Idan ya dauka cewa shi ne ya mallaki ilimin da kansa, wannan tunani yana haifar da girman kai.

4. Kwatanta kansa da waɗanda ba su sani ba
Yana kallon wanda bai sani ba a matsayin ƙasa da shi. Wannan comparison ɗin yana ciyar da girman kai a hankali.

5. Rashin tunanin hisabi (accountability)
Idan mutum bai tuna cewa ilimi zai zama tambaya a ranar lahira ba, zai iya amfani da shi wajen ɗaga kansa maimakon gyara kansa.

Gaskiya mai nauyi:
Ilimi na gaskiya yana ƙara maka tawali’u, ba girman kai ba. Duk lokacin da ilimi ya ƙara girman kai, to akwai matsala a zuciya, ba a ilimin ba.

23/08/2026

•A da ɗalibi idan ya zauna gaban malami, neman ilimi da tarbiyya yake yi.
Yau kuma wasu sun koma neman followers da viral clips.

•Haka wasu malamai sun fi son yawan masoya fiye da yawan masu fahimta.
Idan ka ci gyaran ɗalibi sai ya fusata, idan ka ci gyaran malami sai a ce kana hassada.

•Shi yasa ilimi ya yadu, amma ladabi da gaskiya s**a yi ƙaranci.
Ba duk mai magana bane malami, ba kuma duk mai sauraro bane ɗalibi.

•Barkan mu da dare♥️🥰

Ku Dogara Da Allah 🤲🏽Ku dogara da Allah, kada ku bari tsoro ko damuwa su rinjaye ku. Allah ya ce:﴿أَلَا إِنَّ أَوْلِيَاء...
21/08/2026

Ku Dogara Da Allah 🤲🏽

Ku dogara da Allah, kada ku bari tsoro ko damuwa su rinjaye ku. Allah ya ce:

﴿أَلَا إِنَّ أَوْلِيَاءَ اللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ﴾

“Ku saurara! Lalle masoyan Allah, babu tsoro a kansu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba.”
(Suratul Yūnus: 62)

Idan ka dogara ga Allah da gaskiya, ka sani cewa babu wani abu da ya fi ƙarfin ikonsa. Ka yi haƙuri, ka yi addu’a, ka ci gaba da kyautatawa—Allah ba zai taɓa tozarta mai dogaro da Shi ba. 🤲🏽❤️

Allah Ya sa mu kasance cikin Auliya’unsa. AmiAr-raihaan Multimediaedia

21/08/2026



Abun kirki tun a duniya yake da dadi b***e anje lahira, in ka duba social media jiya zuwa yau, cike suke da hotunan yan ...
20/08/2026

Abun kirki tun a duniya yake da dadi b***e anje lahira, in ka duba social media jiya zuwa yau, cike suke da hotunan yan takaran Najeriya da s**ayi fice a gasar karatun Alqur'ani na duniya, saboda sunyi abun kirki kowa sai murna yake, kowa yana sa albrka da fatan alheri, kowa yana so a danganta shi dasu saboda sunyi abun kirki.

Inda abun banza s**ayi kowa zakaga yana tirr yana nesanta kansa dasu, don sunyi abun banza, to har lahira haka ne, duk wanda yayi abun kirki zaizo yana murna yana nuna takardarsa ya samu pass zaije Aljannah wanda yayi na banza kuma zai rinka boyewa don yasan makomarsa babu kyau..

Allah kasa mu zama na kirki a duniya da lahira.

Hafiz Nafiu Usman Ibrahim ✍️

Address

T/wada
Dukku

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ar-raihaan Multimedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share