TRN HAUSA

TRN HAUSA TRN HAUSA Kamfanin dillacin labarai ne ƙarƙashin Kamfanin Trust And Reality Network (TRN GLOBAL)zaku iya tuntubar mu a wannan lamba: 07071446507
(1)

Ba Tinubu Ne Kaɗai Ya Taka Rawa Wajen Nasarar Buhari A 2015 Ba — AmaechiTsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya musan...
24/05/2026

Ba Tinubu Ne Kaɗai Ya Taka Rawa Wajen Nasarar Buhari A 2015 Ba — Amaechi

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya musanta iƙirarin Shugaba Bola Tinubu cewa shi ne ya fi kowa taka rawa wajen tabbatar da nasarar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a zaɓen shekarar 2015.

Dakarun sojin ƙasar Saudiyya sun yi atisayen tsaro yayin da ake shirin fara aikin Hajjin bana.
22/05/2026

Dakarun sojin ƙasar Saudiyya sun yi atisayen tsaro yayin da ake shirin fara aikin Hajjin bana.

A WANI MATAKI NA BUNKASA ILIMI A KANO: ƊAN BELLO DA UBEC SUN GYARA MAKARANTAR KIMIYYA DA LISSAFI TA KADAWADaga Wakilinmu...
22/05/2026

A WANI MATAKI NA BUNKASA ILIMI A KANO: ƊAN BELLO DA UBEC SUN GYARA MAKARANTAR KIMIYYA DA LISSAFI TA KADAWA

Daga Wakilinmu

An yaba matuƙa ga shahararren ɗan gwagwarmaya, Ɗan Bello, bayan haɗin gwiwarsa da Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Ƙasa wato UBEC wajen gyara Makarantar Firamare ta Musamman da ke koyar da Kimiyya da Lissafi a yankin Kadawa da ke Jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa gyaran makarantar ya haɗa da inganta azuzuwa, samar da yanayi mai kyau ga ɗalibai da malamai, tare da ƙara wa makarantar armashi domin bunƙasa ilimin zamani musamman a fannin kimiyya da lissafi. Kadawa na ɗaya daga cikin yankunan Kano da ke da muhimmanci wajen ci gaban ilimi da noma a jihar.

Al’umma da dama sun bayyana wannan aiki a matsayin abin a yaba, suna masu cewa irin wannan gudunmawa ce ke taimakawa wajen gina makomar matasa da rage matsalolin rashin ingantaccen muhalli a makarantu.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa gyaran makarantar zai ƙara wa yara ƙwarin gwiwar zuwa makaranta tare da samun ilimi cikin walwala da natsuwa.

A nasa bangaren, wani malami daga yankin ya ce:
“Idan aka ci gaba da irin wannan aiki, babu shakka ilimi zai samu babban ci gaba a Kano.”

Yanzu dai mutane da dama na ci gaba da yi wa Ɗan Bello fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya saka masa da alkhairi, Ya ƙara masa lafiya da ikon ci gaba da taimakon al’umma musamman a ɓangaren ilimi da ci gaban matasa.

20/05/2026

Yadda wata babbar motar dakon kaya ta ƙwace ta yi kan mutane a yankin Jihar Gombe.

Arsenal ta lashe kofin ne bayan Man City ta yi canjaras 1-1 a wasanta da Bornemouth a yau Talata. Wannan ne karon farko ...
19/05/2026

Arsenal ta lashe kofin ne bayan Man City ta yi canjaras 1-1 a wasanta da Bornemouth a yau Talata.

Wannan ne karon farko da Arsenal ta lashe kofin tun 2004 ƙarƙashin jagorancin Arsene Wenger.

Yaya kuke ji da wannan labari?

Sadiya Umar Farouq na fama da rashin lafiya a ƙasar Egypt - LauyaTsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq,...
19/05/2026

Sadiya Umar Farouq na fama da rashin lafiya a ƙasar Egypt - Lauya

Tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq, ta kasa gurfana a gaban kotu saboda rashin lafiya, k**ar yadda lauyanta Oladipo Okpesheyi ya bayyana.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, lauyan ya shaida wa babbar kotun babban birnin tarayya da ke Apo cewa Farouq tana kasar Egypt domin jinya, kuma likitoci sun tabbatar da cewa ba za ta iya bayyana a kotu ba sai bayan kusan watanni biyu.

Hukumar EFCC tana tuhumar Farouq tare da Bashir Nura Alkali da wani Sani Mohammed kan laifuka 21 da s**a hada da cin amanar aiki da karkatar da kudade. Hukumar ta zarge su da handame kusan dala miliyan 1.3 da kuma naira miliyan 746.6.

A zaman kotun na ranar Litinin, lauyan EFCC, Rotimi Jacobs (SAN), ya bukaci kotu ta ci gaba da aiki da sammacin k**a Farouq saboda rashin bayyana a kotu. Alkalin kotun, Jude Onwuegbuzie, ya nuna rashin jin dadinsa kan jinkirin shari’ar tare da gargadin cewa za a dauki karin mataki idan ba ta gurfana a zama na gaba ba.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga Yunin 2026 domin fara karanta tuhume-tuhumen.

PANTAMI YA JANYE DAGA TAKARAR GWAMNAN GOMBE A APCTsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da j...
19/05/2026

PANTAMI YA JANYE DAGA TAKARAR GWAMNAN GOMBE A APC

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Gombe.

Pantami ya bayyana cewa ya dauki matakin ne saboda abin da ya kira karya dokar zabe ta 2026 da kuma rashin gaskiya a tsarin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Ya ce duk da biyayyarsa ga APC da bin dukkan ka’idoji, jam’iyyar ta gaza samar masa da muhimman bayanai da hanyoyin da s**a dace domin gudanar da sahihin zabe.

Pantami ya kuma nuna damuwa kan yadda aka gudanar da zabukan fidda gwani na ‘yan majalisar dokoki a jihar, inda ya ce ba a bai wa magoya baya da wakilai damar shiga yadda ya k**ata ba.

Ya gode wa matasa da magoya bayansa, musamman wadanda s**a tara kudaden sayen fom dinsa ta hanyar gudunmawa, tare da kira ga mabiyansa da su kasance masu bin doka da oda.

Kungiyar Pantamiyya Movement ta ce za ta sanar da matakin da za ta dauka nan gaba a fagen siyasa.

Da Ɗumi-ɗumi: An Kai Wa Tinubu Rahoton Cewa Ina Ƙoƙarin Kashe Shi — ShettimaMataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim S...
19/05/2026

Da Ɗumi-ɗumi: An Kai Wa Tinubu Rahoton Cewa Ina Ƙoƙarin Kashe Shi — Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa wasu mutane sun kai wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, rahoton cewa yana ƙoƙarin kashe shi watanni kaɗan bayan hawansu mulki.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan yadda wasu s**a yi yunƙurin haddasa rashin jituwa tsakaninsa da shugaban ƙasar, yana mai cewa Tinubu bai yarda da irin waɗannan zarge-zarge ba.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce akwai wasu mutane da s**a yi ƙoƙarin haifar da rabuwar kai tsakanin shugabannin biyu, amma duk da haka dangantakarsu ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi.

Kalaman na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa a fagen siyasar Najeriya kan alaƙar da ke tsakanin manyan jagororin gwamnatin tarayya.

Hukumar tace fiina-finai ta Kano ta jagoranci wasu mata uku zuwa karɓar addinin MusulunciHukumar Tace Fina-finai da Dab’...
19/05/2026

Hukumar tace fiina-finai ta Kano ta jagoranci wasu mata uku zuwa karɓar addinin Musulunci

Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta jagoranci wasu mata uku masu sana’ar wasan Gala zuwa ga karɓar addinin Musulunci bayan sun nuna ra’ayinsu na rungumar addinin da kansu.

A wata sanarwa da Hukumar ta fitar ranar 19 ga watan Mayun 2026, ta ce an gudanar da taron ne cikin wani biki na farin ciki da aka shirya a harabar dakin taron Hukumar, inda shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha, ya jagoranci matan wajen karɓar addinin Musulunci.

Shugaban Hukumar ya bayyana ranar a matsayin daya daga cikin ranakun da s**a fi ba shi farin ciki a rayuwarsa, yana mai cewa shawarar da matan s**a yanke ta samo asali ne daga kyawawan halaye, zaman lafiya da kuma mu’amala ta gari da s**a gani daga abokansu Musulmi a masana’antar nishadi.

Sanarwar ta ce matan ukun da s**a karɓi Musuluncin sun hada da Dicson da Zara daga Jihar Adamawa, sai Hannatu daga Jihar Gombe, wadanda s**a dade suna gudanar da sana’ar Gala a Kano.

Matan sun bayyana jin dadinsu kan matakin da s**a dauka, tare da godewa irin kauna da kyakkyawar mu’amala da s**a samu daga abokansu da sauran jama’a a Kano.

Da take jawabi a madadin wadanda s**a karɓi Musulunci, Hannatu ta ce kyawawan koyarwar addinin Musulunci da yadda Musulmai ke rayuwa cikin zaman lafiya da kyautatawa juna ne s**a yi tasiri wajen yanke shawarar rungumar addinin.

Sanarwar ta samu sa hannun Abdullahi Sani Sulaiman a madadin shugaban Hukumar.

Da Ɗumi-ɗumi: EFCC Ta Cafke Tsohon Minista Mamman Saleh a KadunaHukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa, Economic a...
19/05/2026

Da Ɗumi-ɗumi: EFCC Ta Cafke Tsohon Minista Mamman Saleh a Kaduna

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki, Mamman Saleh, a jihar Kaduna State.

Rahotanni sun ce an k**a shi ne a unguwar Rigasa da ke cikin birnin Kaduna a ranar Talata, yayin da jami’an hukumar s**a gudanar da aikin kamen cikin sirri.

Sai dai har zuwa yanzu hukumar EFCC ba ta fitar da cikakken bayani kan dalilin kamen ba, amma ana sa ran za ta bayyana karin haske cikin sa’o’i masu zuwa.

An bayyana cewa Mamman Saleh ya taba rike muƙamin Ministan Wutar Lantarki a gwamnatin tarayya kafin ya bar mukaminsa.

A bangaren bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta kuwa, ana danganta shi da wata shari’a da ta kai ga hukuncin da ake yadawa, sai dai har yanzu ba a samu tabbaci daga hukumomi kan hakan ba.

Martanin Gwamnan Kano Ga Kwankwaso Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da martani mai kaushi ga tsohon ubangi...
19/05/2026

Martanin Gwamnan Kano Ga Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da martani mai kaushi ga tsohon ubangidansa.

Gwamnan ya bayyana cewa biyayya ce ta sa ya rika daukar wasu maganganu cikin natsuwa, amma ya gargadi cewa idan babba bai rike bakinsa ba, to “yaro ma zai iya bude bakinsa.”

Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sabanin siyasa tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar Kano, musamman tsakanin bangarorin da ke da alaka da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin wannan furuci na iya kara nuna tashin hankali a dangantakar siyasar cikin gida a jihar, duk da kokarin da ake yi na rage rikice-rikicen siyasa a Kano.

Address

Dutse

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TRN HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share