Online radio zamani fm dutse

Online radio zamani fm dutse Labaran duniya

06/07/2026

05/7/26 IZALA
An shawarci al'ummar Musulmi su yi aiki da koyarwar Alkur'ani Mai girma da Hadisan manzon tsira SAW wajen gudanar da ibada da Kuma rayuwar su ta yau da kullum.
Sheikh Sabo Musa Hassan ne yayi wannan bukatar a lokacin da yake gabatar da nasiha Mai Taken riko da Sunnah Bidi'a Sam ga daruruwan musulmi a masallacin Sunnah na garin Kila a yankin K/H Gwaram.
Sheikh Sabo Musa Hassan Katsina Wanda Kuma shi ne Mai bawa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan al'amuran addini, ya ce aiki da koyarwar Alkur'ani mai girma da Hadisan manzon tsira, ita ce hanyar samun rahama ga kowane musulmi a duniya.
Malamin Wanda ya dauki lokaci Mai tsawo ya na karanto ayoyin Alkur'ani Mai girma da Hadisai, ya hori al'ummar musulmi su guji Sanya bidi,'oi cikin addini domin gudun gamuwa da fushin Allah a ranar lahira.
Sheikh Sabo Musa Hassan Katsina Wanda har wayau shi ne Sakataren kungiyar IZALA na Jihar, ya bukaci musulmi, musamman Matasa su tashi tsaye wajen neman ilimin addini domin kaucewa fadawa cikin bidi'oi da sunan addini.
Tun farko sai da babban Limamin masallacin Sunnah na Gwaram-Sabuwa, Ustaz Adamu Isah ya gabatar da malamin tare da wadanda suke rufa masa baya.

10/05/2026

Barkan mu da Wannan rana yan uwa masu albarka kuna tare da tashar yanci ta online radio zamani fm dutse a Wannan Lokaci.

Ku turo sakon barka da hutun karshen mako zuwa ga yan uwa da abokan arzukin.

Address

New Market Street
Dutse
6-6

Telephone

+2349128097919

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Online radio zamani fm dutse posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Online radio zamani fm dutse:

Shortcuts

Share