21/04/2025
Raddi Dangane da Manufofin Bola Tinubu na 2027:
Ashe har yanzu dai ana ƙoƙarin raina hankalin ‘yan Najeriya da ƙoƙarin sake shuka ciyawar da ta hana ƙasa girma! Bola Ahmed Tinubu, wanda har yanzu bai iya cika alƙawurran da ya ɗauka a 2023 ba, yana ƙoƙarin sake fitowa da wata sabuwar lissafa ta manufofi guda 8, wai don neman tazarce a 2027. To amma muna tambaya: Me ya cika daga cikin manufofin da ya gabatar a farko? Shin muna mantawa da sauƙin da aka yi alkawarin kawo wa rayuwar talaka? Ko kuma muna shirin sake yarda da kyandir din da ya ƙone sau ɗaya?
Wai “Food Security”, amma ‘yan Najeriya suna ta shiga layi don samun buhun shinkafa a farashin da ya zarce ƙarfin mai albashi? “Ending Poverty”, alhali talauci ya narke cikin jinin kowane talaka a ƙasar nan – da kyar ake iya cin abinci sau ɗaya a rana. “Job Creation”, amma matasa sai su ɗauki shaidar digiri su je su sayar da goro a t**i?
Ana ce “Access to Capital”, amma an kasa saukaka bashi ko tallafin da zai sa matasa su farfaɗo da sana'o'insu, sai dai manyan ‘yan siyasa ke ci su sha. “Improving Security”? A wane yanki? Najeriya ce ta fi hatsari yanzu – daga Arewa maso Yamma har zuwa Kudu maso Gabas, babu wanda ke cikin kwanciyar hankali.
“Rule of Law”? To me ya hana a hukunta manyan barayin gwamnati da aka bankado cikin man fetur, kwangila, da kuɗin kasafin kudi? Sai dai a cafke talaka idan ya saci burodin raƙumi. “Fighting Corruption”? Wannan kuma dariya ce. Ya kamata mu fara da inda kuɗaɗen man fetur s**a shige, da kuma waɗanda s**a lalata naira har ta zama tamkar takardar wanka.
Mu faɗa a fili: ’Yan Najeriya ba mahaukata ba ne. Mun farka. Ba za mu sake yarda da gyara da bakar wuƙa ba. Idan da gaske Bola Tinubu na son komawa mulki, to sai ya fara cika alƙawurran da ya ɗauka a 2023 – ko kuwa kawai yana ƙoƙarin ci gaba da jefa ƙasa cikin rami mai zurfi da babu fita.
A 2027, Najeriya tana buƙatar sabuwar ƙwaƙwalwa, sabuwar zuciya, da sabuwar ƙaƙƙarfan jagoranci – ba kwafin wanda ya gaza a darasi na farko.