
08/08/2025
08-08-2025 FULATA
Hadimin wakilin mazabar Kirikasamma da Guri da kuma Birniwa a majalissar wakilai ta kasa a karamar Hukumar Birniwa , Musa Muhammad Isyaku Birniwa ya ce an kammala aikin sanya fitilin kan t**i masu amfani da hasken rana a garuruwa 13 daga cikin 15 da ake aikin a karamar Hukumar Birniwa
Ya sanar da hakan ne a lokacin ganawa da wakilinmu ta wayar hannu
Mallam Musa Muhammad Isyaku ya ce an kammala aikin ne a garuruwan Burseli da Jirgiwa da Matamu da sabbin unguwannin Birniwa da Maiso da cikin garin Diginsa da Jirgiwa da Matamu da Kibu da Laraba da Tsangaya Yamma
Ya ce aiyukan da s**a rage guda biyu sune na garuruwan Matarar Batu da kuma Kubuna
Hadimin na dan majalissar a karamar Hukumar Birniwa yana mai cewar ana gudanar da aiyukan ne domin kawata gari da kuma inganta al’amurran tsaro
Ya ce aiyukan na daga cikin aiyukan mazabu na dan majalissar tarayya Honourable Abubakar Hassan Fulata.
Musa Muhammad Birniwa ya kuma ce ana gudanar da irin wadannan aiyuka a dukkanin kananan hukumomin uku na mazabarsa
Dan majalissar ya kuma gina sabon masalacin kamsisalawati a garin Masewa dake mazabar Karanka da gina ajujuwan karatu shida a garin Fulatanan domin karantar da yara
Haka kuma dan majalissar ya raba kayayyakinh kimiyya da littattafai na kimiyya ga daliban yankin