20/09/2024
ƘUDURORIN MAJALISAR ZARTASWA TA JIHAR JIGAWA
(19 ga Satumba, 2024)
Majalisar ta amince da:
(1) AYYUKAN FANNIN ILIMI: An amince da bayar da ware kuɗi har N2,559,384,928.49 don bayar da kwangilar ayyukan gini, gyara, sayen kayan aiki da tsaftar makarantun firamare a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Haka kuma, an amince da ware kuɗi har Naira N1,053,728,600.16 don bayar da kwangilar gyaran makarantu na firamare da ƙananan makarantun sakandare waɗanda iska ta lalata a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
(2) CIBIYAR HORAS DA ƊALIBA TA ICAN: Sanya hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar horas da ɗalibai ta musamman wadda ƙungiyar ƙwararrun akantoci ta Najeriya (ICAN) za ta gina a birnin Dutse a matsayin haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar ta ICAN da Gwamnatin Jihar Jigawa.
(3) SAMAR DA KAYAN AIKIN NOMA: An amince da ware kuɗi har Naira N26,274,553,600.00 don sayen tantan ɗin noma guda 300, garmar huɗa guda 300, garmar noma guda 300, garmar tada kunya (disc ridger) guda 300, Bodin tantan (Tipping Trailer) guda 300, injin shuka guda 150, injin shukar shinkafa guda 150, motar girbin amfanin gona guda 40, da kuma na’urar feshin maganin ƙwari guda 80.
Haka kuma an ware Naira Miliyan 263,160,000 don tura ma’aikata 30 zuwa ƙasar China don samun horo na tsawon watanni uku kan yadda za su riƙa kula da kuma gyaran sababbin na’urorin da za a samar.
Za a kafa cibiyoyi 60 da za a ajiye waɗannan kayan aiki a faɗin jihar, inda za a samar da cibiyoyi biyu a kowacce daga mazaɓun ‘yan majalisar jiha guda 30, sannan kowanne ɗaya daga cikin waɗannan ƙwararrun ma’aikata zai riƙa kula da cibiyoyi biyu.
Wannan shiri zai samar da ayyuka yi ga matasa 2,700, kuma zai ƙara yawan ayyukan yayin da aikin ke cigaba.
(4) SAMAR DA KUƊI: Majalisar ta amince da sakin kuɗi har Naira N8,194,918,000.00 don biyan kaso 30% na kuɗin kayan aiki da kuma horar da malaman gonar guda 30.
Government House Press.