23/10/2024
Duba da irin yanayin da ake ciki na yawaitar zazzabin maleria da ke addabar al'uma, Dan takardar shugabancin karamar hukumar Gwale a karkashin inuwar jam'iyyar NNPP Hon. Abubakar Mu'azu (MOJO) babban amin dan takarar Mustapha Iyali Abdullahi (QUANTY) ya bullo da wani shiri mai taken Mojo Care, cikin shirin suna raba wa marasa kafin da ke fadin karamar hukumar magunguna tare da yi musu gwaje-gwaje akan cutukan maleria, da typhoid, da blood pressure, da ciwon hakori, da kuma gudawa, inda bayan tabbatar abin da ke damun mutum za a ba shi magani kyauta, Tsarin na kewaya wa dukkan mazabun da ke karamar hukumar domin cin moriyar sa ga mata, da maza, da yara da kuma manya.
Shirin ya sami karbuwa a duk fadin karamar hukumar ta Gwale, inda al'uma ke yin tururuwa suna karbar magungunan da kuna godiya da sa albarka.
A jawabinsa yayin gudanar da shirin Hon. Mojo ya tabbatar wa yan karamar hukumar Gwale cewa hakan so in tabi ne idan har Allah ya ba su nasara a wannan zabe mai zuwa lallai yanzu aka fara samun ribar dimokaradiiya.
A karshe ya yi kira ga al'umar jihar Kano da su yi zabe cikin kwanciyar hankali tare da bin doka da oda.