Jigawa Times TV

Jigawa Times TV Jigawa Times TV is an online Channel providing you with latest news and informative programmes.

Wani jami’in rundunar sojin Najeriya mai mukamin Kanal, Abdusalam Ude, ya rasa ransa a Abuja bayan wasu da ake zargin ma...
29/07/2026

Wani jami’in rundunar sojin Najeriya mai mukamin Kanal, Abdusalam Ude, ya rasa ransa a Abuja bayan wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne s**a yi yunkurin sace shi.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da maharan s**a tare Kanal Ude tare da kokarin yin garkuwa da shi. Sai dai jami’in sojan ya yi yunkurin hana su aiwatar da shirin nasu, lamarin da ya kai ga harbe shi har lahira.

Majiyoyi sun ce matar mamacin da direbansa sun samu raunuka sakamakon harbin da maharan s**a yi yayin kai harin, kuma ana ci gaba da kula da su a asibiti.

Wannan lamari ya sake jefa al’umma cikin fargaba tare da tayar da hankula kan tabarbarewar matsalar tsaro a Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda a baya ake kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da s**a fi tsaro a Najeriya.

Me zaku ce?

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya karrama manyan jami’an ’yan sanda 30 da aka yi wa k...
21/07/2026

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya (IGP), Olatunji Rilwan Disu, ya karrama manyan jami’an ’yan sanda 30 da aka yi wa karin girma zuwa mukaman Mataimakan Sufeto Janar (AIG) 13 da Kwamishinonin ’Yan Sanda (CP) 17.

An gudanar da bikin ne a dakin taro na Goodluck Ebele Jonathan Peacekeeping Hall da ke Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa a Abuja.

A jawabinsa, IGP Disu ya taya jami’an murnar karin girman, yana mai cewa sabon mukamin da s**a samu na nufin karin nauyi da alhakin jagoranci. Ya yabawa jajircewarsu da sadaukarwar da s**a yi tsawon shekarun aikinsu, tare da godewa iyalansu bisa irin goyon bayan da s**a ba su.

Sufeto Janar din ya bukaci sabbin jami’an da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, adalci da tausayi, tare da fifita jin dadin jami’an da ke karkashinsu da kuma karfafa amincewar jama’a ga rundunar ’yan sanda. Haka kuma ya bukace su da su kasance abin koyi ga matasan jami’ai masu tasowa.

Bikin ya samu halartar manyan baki daga gwamnati, hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya, ciki har da Mataimakin Gwamnan Jihar Cross River, wakilan gwamnonin Jigawa da Anambra, da kuma shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Hali ta Kasa.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta jaddada kudurinta na ci gaba da kula da walwalar jami’anta, bunkasa kwarewarsu da kuma inganta ayyukan tsaro domin samar da runduna mai gaskiya da rikon amana.

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Shalkwata da ke Jos ta kai ƙarar fitaccen matashin ...
21/07/2026

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen Shalkwata da ke Jos ta kai ƙarar fitaccen matashin mawaƙi, Usman Umar, wanda aka fi sani da Soja Boy, wajen mahaifiyarsa bisa zargin yin kalaman da s**a shafi shugaban ƙungiyar, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir.

Rahotanni sun nuna cewa wata tawaga daga ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin shugaban matasa na reshen jihar Sokoto, ta kai ziyara gidan mahaifiyar mawaƙin da ke unguwar Runjin Sambo a birnin Sokoto. Tawagar ta bayyana mata kalaman da ake zargin ɗanta ya yi game da Sheikh Jingir tare da bayyana matsayar ƙungiyar kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da kwamitin yaɗa labarai na JIBWIS ya fitar, ƙungiyar ta ce tawagar ta gabatar da cikakken bayani kan lamarin tare da nuna damuwarta kan kalaman da aka danganta ga Soja Boy.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa mahaifiyar mawaƙin ta nuna damuwa bayan jin bayanan da aka gabatar mata, yayin da ƙungiyar ta sake jaddada rashin amincewarta da duk wasu kalamai da za su iya zubar da mutuncin malamanta da shugabanninta.

Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Soja Boy bai fitar da wata sanarwa a hukumance ba domin mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi masa.

Me zaku ce?

18/07/2026

Kungiyar APC ACTION GROUP ta jihar Jigawa ta sake jaddada goyon bayanta ga jam'iyyar APC.

17/07/2026

Titin Jirgin kasa kenan da ake kan aikinsan Wanda ya tashi daga Kano zuwa Maradi Wanda yakasance wani bangarene na ayyukan titunan da shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu ya bayar ayi.

17/07/2026

Malam Umar Namadi bashi ke bada takara ba Allah ne, wadanda Allah ya Basu abaya akazo aka hadu aka taimaka musu s**aci zabe, to suma yakamata suzo ahadu dasu domin su rama biki bawai sufice daga Jamiyya ba, indai domin Alumma sukeyi.

Ku saurari Shira kashi na Biyu tareda:
Hon Musa Shuaibu Muhammad Guri (Coordinator na Renewed Hope Ambassadors) Jigawa State Chapter.

Shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu yanada tarin ayyuka a Jihar Jigawa, Hon Musa Shuaibu Muhammad Guri. Ku biyomu domin kawo...
16/07/2026

Shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu yanada tarin ayyuka a Jihar Jigawa,
Hon Musa Shuaibu Muhammad Guri.

Ku biyomu domin kawo muku Shira ta musamman tare da Hon Musa Shuaibu Muhammad Guri, Coordinator na Renewed Hope Ambassadors Jigawa State.

Tasha ɗaya tilo a shafukan sada zumunta dake kawo mu ku zafafan rahotanni kai tsaye daga lunguna da saƙuna na ciki da Wa...
16/07/2026

Tasha ɗaya tilo a shafukan sada zumunta dake kawo mu ku zafafan rahotanni kai tsaye daga lunguna da saƙuna na ciki da Wajen jihar Jigawa dama sassan duniya baki ɗaya.

Muna yi muku fatan alkhairi dafatan kuma cikin koshin lafiya.

Shin daga ina kuke kasancewa damu?

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu a bangaren ta bata  haramta sana’ar downloading...
16/07/2026

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu a bangaren ta bata haramta sana’ar downloading ba a faɗin jihar, tana mai jaddada cewa har yanzu ba ta soke wannan sana’a ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, hukumar ta bayyana cewa babu wata shawara ko mataki da ta ɗauka na dakatar da sana’ar, duk da wata sanarwa da ta bazu a kafafen sada zumunta.

Hukumar ta ce tana gudanar da bincike kan wani saƙon murya da ke zargin wasu masu downloading da yaɗa bidiyoyin batsa, inda binciken farko ya nuna cewa muryar da ke cikin saƙon ba ta fito daga Kano ba, sai dai an ci gaba da zurfafa bincike.

Ta kuma bayyana cewa ta tura jami’anta zuwa dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar domin gano da kuma dakile duk wani abu da ya saɓa wa doka da tarbiyya.

Hukumar ta ƙara da cewa sana’ar downloading na taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi ga matasa da bunƙasa masana’antar Kannywood, saboda haka babu shirin soke ta.

Sai dai ta yi gargaɗin cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu yana amfani da sana’ar wajen yaɗa abubuwan da s**a saɓa wa doka, tarbiyya da koyarwar addinin Musulunci.

Address

Maifulani Plaza Along Kwanar Huguma Road
Dutse

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jigawa Times TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category