Taska Multimedia

  • Home
  • Taska Multimedia

Taska Multimedia Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Taska Multimedia, Media/News Company, Bwari Abuja sabo Gari Road, .

ALHAMDULILLAH
15/02/2026

ALHAMDULILLAH

14/02/2026
"Alhamdu lillah! Barka da wannan rana mai albarka, ranar Jumma'a. Allah ya sanya wannan rana ta zama silar bude mana kof...
06/02/2026

"Alhamdu lillah! Barka da wannan rana mai albarka, ranar Jumma'a. Allah ya sanya wannan rana ta zama silar bude mana kofofin alheri, ya bamu ikon cin moriyar wannan rana, ya kuma karbi ayyukanmu na kwarai. 🌙🤲

Allah ya kare yankunanmu da kasarmu daga dukkan fitinu. Barkarku da Jumma'a mabiya Taskar Multimedia!"

05/02/2026

**LABARI DA DUMI-DUMI: Tashin Hankali a Jihohin Kwara da Katsina**

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Wani mummunan rahoto da muke samu yanzu-yanzu daga kafar yada labarai ta **Al-Jazeera** ya tabbatar da cewa yan bindiga sun karkashe kusan mutane 200 a wasu hare-hare na rashin imani da s**a kai a sassan jihohin **Kwara** da **Katsina**.

Wannan hari ya zama mafi muni da aka taba gani a wadannan yankuna cikin watanni da dama, kuma yana zuwa ne a daidai lokacin da kasar take fama da fadada kalubalen tsaro daga bangaren yan tada kayar baya da gungun yan fashin daji.

**Allah Ya Kawo Mana Karshen Wannan Masifa:**
Muna rokon Allah ya jikan wadanda s**a rasu, ya ba wa iyalansu hakurin jure wannan rashi, ya kuma tabbatar mana da zaman lafiya a kowace kusurwa ta Najeriya. Amin.

**Ku Biya Mu:**
Domin kallon bidiyon wannan rahoto da sauran cikakkun bayanai, ku kasance da mu a wannan shafi na **Taskar Multimedia**.

04/02/2026

“Duk wani ɗan siyasan da ya ce ku zo ku yi bangan siyasa, ku ce masa shi ma ya fito da ɗansa. Kada ku yarda a yi amfani da ku a siyasa a kawo rashin zaman lafiya” - Gwamna Uba Sani

Rashin Ilimi ke kawo Auren wuri ga Mata A Arewacin Najeriya -Sarki Muhammadu Sanusi. Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ...
04/02/2026

Rashin Ilimi ke kawo Auren wuri ga Mata A Arewacin Najeriya -Sarki Muhammadu Sanusi.

Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya ƙalubalanci duk wani ra’ayi da ke ganin al’ada na ba da damar a duka mata ko a yiwa yara cin zarafi. Ya ce al’adu ba su da hurumin saɓani da doka, kuma babu dalili na al’ada da zai sa a ci zarafin mata ko yara.

A wata hira da ya yi da tashar talabijin, Sanusi ya yi kira ga al’umma su fahimci cewa cin zarafi da ake danganta wa al’ada a gaskiya yana fitowa ne daga rashin daidaito na ikon da maza ke da shi, talauci, da gazawar gwamnati wajen samar da makarantu da ayyukan more rayuwa.

Ya ƙara da cewa ba a takaita wannan matsala ga al’umma ɗaya ko yankin da ba na Afrika ba — cin zarafi yana faruwa a kowane wuri, kuma ba al’ada ce da za a runguma ba.

Bugu da ƙari, Sarkin ya ja hankalin jama’a game da auren yara ƙanana musamman a ƙauyuka, yana cewa mutane suna yin hakan ne saboda rashin damar samun ilimi, hanyoyi masu wahalar tafiya, da rashin wuraren koyon sana’o’i, ba saboda al’ada ba.

Ya jaddada cewa dokar Najeriya ta tanadar da kariya ga mata da yara, kuma wajibi ne gwamnati da jama’a su tsaya tsayin daka wajen kare mafi raunana.

04/02/2026

Zancen nagaski wanna Babu shakka ko kowanto Acikin Sha shine Alkiyama

04/02/2026

Allah Ya shiryar dumu Hanyar Ma daidaiciya

Address

Bwari Abuja Sabo Gari Road

TASKAMULTIMEDIA6019

Telephone

+2348169564813

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taska Multimedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Taska Multimedia:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share