
10/08/2025
Labaran Yammacin Lahadi 16/02/1447AH - 10/08/2025CE Ga Takaitattun Labaran.
Hukumar NDLEA ta k**a Fasto da take nema ruwa a jallo kan safarar miyagun kwayoyi a Legas.
Gwamna Abba na jihar Kano ya bai wa dalibai 1,130 kayan aikin sana’o’in hannu.
Hukumar NDLEA ta cafke masu baburan da ke kai saƙon muggan kwayoyi a Abuja.
Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa da kuma kungiyar Editocin Najeriya (NGE) sun maka Gwamnan Jihar Neja Umar Bago da Hukumar Yada Labarai ta Kasa a kotu kan rufe gidan rediyon Badeggi FM.
Wasu mahara sun hallaka mutum 2 tare da ƙona gidaje da kuma coci-coci a karamar hukumar Bokkos na jihar Filato.
Jami’an Hukumar EFCC, sun kai samame a dakin Karatun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda s**a k**a wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne.
Gwamnonin arewa na alhinin mutuwar tsohon ministan noma Cif Audu Ogbeh.
Gwamnan Kano ya karɓi daruruwan ƴan APC da s**a sauya sheka zuwa NNPP.
Kamfanin Oxfam ya fitar da rahotan cewa ƴan Najeriya miliyan 83 ke cikin talauci yayin da kaso 10 cikin 100 ne kacal ke facaka da arziƙin ƙasar.
Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda da jami'an sa kai 13 a jihar Zamfara.
Jihar Kogi ta kafa kotuna 9 don hukunta masu cin zarafin Mata.
An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ƴan bindiga s**a kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra'ila ba ta "zaɓi" illa "karasa aikin" da ta fara wajen ƙarya lagon Hamas.
Kotu ta ɗaure tsohon Firaministan Chadi shekara 20 a gidan yari.
Ana zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza.
Birtaniya za ta fara tisa ƙeyar bakin da s**a aikata laifi zuwa gida.
Ƙawayen Ukraine sun ce dole ne a sa ƙasar a tattaunawar zaman lafiya.
Barau FC dake Kano ta ɗauki 'yanwasa 10 kafin fara firimiyar Najeriya ta bana.
Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa ba tare da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba.
Community Shield: Crystal Palace tayi nasara akan Liverpool daci 3 : 2 a bugun Fanareti bayan tashi 2 : 2 a wasan share fagen kakar 2025/2026 wadda za a fara Juma a mai zuwa.
Newcastle United na gab da kammala ɗaukar ɗanwasan baya Malick Thiaw daga AC Milan.
Sunderland ta ɗauki ɗanwasa na 10 kafin fara kakar wasa ta bana.
Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, ƙungiyar da a bayan nan ke fama da matsalar rashin kuɗi.