04/12/2025
Kuskuren da jam'iyyar APC'N Kano tayi a 2023 Allah yasaka wa Barau shine suke ƙara maimaita shi a wannan lokacin
Idan na tuna abinda ya faru a kakar 2023 tun daga 2020 zuwa kafin zaɓe yadda aka haɗe kai akan dole sai an taɓar da Sanata Barau a jam'iyyar APC'N Kano saina ƙara godewa Allah yanzu kuma nasamu salama saboda yadda takaya dakuma nasarar da Sanata Barau ɗin yasamu Allah yayi masa sakayya da Kujerar Mataimakin shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya lamba biyar a ƙasa gabaɗaya shine suke ƙarayi.
Mai yafaru a wancan lokacin baka isa ka futo kace kai Barau kakeso ba kai zaɓaɓɓe ne, Naɗaɗɗe ne, Shugaban jam'iyya ne ko wanda yake aiki a wata ma'aikata batare da an cima mutunci ba yadda aka haɗe kai duk jam'iyyar taƙi Sanatan bayan a lokacin yafi kowa amfanawa al'umma, jam'iyyar da su kansu shuwagabannin amman hakan baisa sun raga masa ba yazamana cewa sun maidashi ɗan bora su dinga yaƙarsa, kai saida takai idan an kawo kayan arziƙi wa al'umma sai an hana saidai a kai Ofishin Yan sanda a raba amman mai yafaru bayan zaɓen 2023 sune a ƙasa shine a sama.
Shiyasa a duk lokacin da na tuna abunda yafaru a baya zance yanzu don sunyi wannan abun ai bai zama abun mamaki ba, Amman kusani cewa mune yan adawar a Jihar nan muddin kunason nasarar kanku to Wallahi ku rungumi haɗin-kai ayi tafiya tsintsiya maɗauri ɗaya ware Sanata Barau shi kaɗai da ƙinsa Wallahi haƙurinsa Allah bazai taɓa barinku kunyi nasara ba shikuma zaiyita Nasara saboda kyakkyawar zuciyarsa akan kowa.
Kuyi tunani kuma ku tuna!
Young barau jibirin