
13/06/2025
Gamayyar kungiyoyin fararen hula a karamar hukumar Faskari sun yi gangami domin nuna goyan baya ga dikko radda da alwashin siya ma Dikko form da Aminu Barau don fafatawa a zaben 2027
Gamayyar wasu kungiyoyi guna goma cur a karamar hukumar Faskari sun dunkule tare da gudanar da wani gagarumin taro, don nuna goyon bayansu ga Gwamna Malam Dikko Radda, tare kuma da yabawa da kwazon babban mai ba Gwamna shawara a kan ci gaban al'umma Engr Aminu Barau Mairua
Ƙungiyoyin da s**a hada da;
Ƙungiyar Mata Zalla ta Mairua
Ƙungiyar Noma da Kiwo Association
Ƙungiyar Masu Ƙuli-ƙuli
Ƙungiyar Aminu Barau Mobilization Awareness Daudawa
Ƙungiyar Ba Mai Yi Sai Allah
Ƙungiyar Dikko Alheri Organisation
Ƙungiyar 34 LG Awareness In Politics
Faskari Media Team For ABM
Ƙungiyar Aminu Barau Foundation
Ƙungiyar 361 Ward Support and Mobilization Forum
Sun gudanar da taron ne a garin Daudawa, inda s**a cimma yarjejeniyar dunƙulewa tare da kafa wata sabuwar kungiyar da za su yi aiki tare mai suna Dikko 4+4
A lokacin ƙaddamar da taron ƙungiyar ta bayyana cewa bisa yadda s**a fahimci alkairin Gwamna Dikko Radda sun fi kurakuransa yawa a Katsina, don haka sun aminta da ya zarce, sannan kuma za su saya masa fom din takara kyauta, daga nan zusa farkon shekarar 2026
Haka kuma kungiyar ta bayyana cewa bayan ta sai ma Gwamna fom din takarar gwamna, za kuma ga sai ma Engr Aminu Barau Mairua fom din takara, da shi ma za a fafata da shi a zaben 2027, don samar da wakilci na gari ga al'ummar wannan shiya