
22/07/2025
MINISTAN MATASA....
Daga Rabiu Biyora
Ganin irin yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tsaya tsayin daka wajen jana'izar marigayi tsohon Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari da kuma kyakkyawar alakar dake tsakanin Buhari da Tinubu sai nake ganin abu ne mai kyau a siyasa Shugaba Tinubu ya bawa Yusuf Buhari mukamin Minista musamman Ministan Matasa...
Yin hakan zai kara dankon zumunci sosai...
A yanzu Yusuf Buhari yana da shekara 33 a duniya shekarun da zasu bashi damar tsayawa kowacce irin takara a Nigeria...
A bangaren siyasar Arewa kasancewar Yusuf Buhari minista a gwamnatin Tinubu hakan zai iya zama dalilin da Tinubu zai samu karin magoya baya daga yankin Arewa Maso Yamma.....