
05/01/2023
AlhamdulilLah
A Yau Laraba 4/1/2023 Na Jagoranchi Ƙaddamar Da Buɗe Taron Ƙarawa Juna Sani Wanda Ƴan A'gajin Ƙungiyar Mu Mai Albarka FIRST AID GROUP FITYANUL ISLAM OF NIGERIA Ƙarƙashin Jagorancin(CODASU UNIT) Wato Ɓagarenta Na Yaƙi Da Ƙananan Cututtuka Ta Shirya Na Kwana 3 A Nan HAJJ CAMP Dake Babban Birnin Tarayya ABUJA Yayinda Na Gabatarwa Mahalartan Muhadarata Mai Taken ( MA'ANAR FITYANUL ISLAM DA ABUBUWAN DA SUKE WAJABA AKAN MEMBOBINTA).
Muna Yiwa Dukkannin Mahalarta Fatan Alkhairi Muna Yiwa Kowa Addu'a Yadda Aka Fara Wannan Seminar Lafiya Allah Yasa A Gama Lafiya Albarkar Shugaba Sallallahu Alaihi Wa A'lihi Wa Sallama.
Zanyi Amfani Da Wannan Damar In Gayyaci Dukkannin Membobin Mu Halartar Rufe Wannan Seminar Mai Albarka Ranar Lahadi 8/1/2023 Ƙarfe 9:30AM Tara Da Rabi Na Safe A Babban Ɗakin Taro Na Babban Masallacin Ƙasa Central Mosque,Abuja.
Allah Ya Bada Ikon Zuwa Ameen.
Al-murabbi Al-barnawi
Chairman Fityanul Islam Of Nigeria Fct Abuja Branch
Fityanul Islam TV