29/01/2026
SaĆon Godiya Daga Al'ummar Garin TumÉurkai Zuwa Ga A.A Albasu
A ranar 21 ga watan Janairu, 2026, alâummar garin TumÉurkai ta bayyana muradinta cikin mutunci da girmamawa ta hanyar rubutu da na wallafa a wannan fej Éin nawa da yawun al'ummar garin TumÉurkai, wanda ya shafi aikin sanya fitilun t**i da A.A. Albasu ya kawo domin haskaka garin TumÉurkai. SaĆon ya fito ne ba da zargi ko Ćalubale ba, sai dai a matsayin roĆo na alâumma mai cike da godiya da fatan alheri.
Abin farin ciki da Ćarfafa gwiwa shi ne, saĆon bai tafi a banza ba. Bayan wallafa rubutun, na samu sahihan bayanai daga makusanta da masu kusanci da A.A. Albasu cewa saĆon ya isa gare shi, ya kuma karÉe shi da kyakkyawar fahimta. Haka kuma, an bayyana min cewa ya ji koken alâumma, kuma cikin yardar Allah, nan ba da jimawa ba za a ci gaba da aikin sanya fitilun domin su zama abin morewa ga mutanen da aka yi niyya domin su tun farko.
Wannan lamari ya sake tabbatar da muhimmancin magana cikin hikima, da amfani da kafar sadarwa ta hanya mai kyau wajen isar da saĆon alâumma. Ya nuna cewa idan aka yi magana da hujja, ladabi da girmamawa, tana iya samar da sakamako mai kyau fiye da hayaniya ko faÉa. Haka kuma, ya nuna cewa akwai shugabanni da masu hannu da shuni da ke sauraron jamaâa, kuma ke Éaukar irin waÉannan kira da muhimmanci.
Mu alâummar TuÉurkai muna miĆa babbar godiya ga A.A. Albasu bisa yadda ya karÉi wannan kira, da yadda ya nuna cewa har yanzu zuciyarsa tana tare da jamaâarsa. Wannan amsa da aka samu ta Ćara wa jamaâa kwarin gwiwa, ta kuma Ćarfafa alaĆar fahimta da amincewa tsakanin alâumma da masu hidima.
Muna adduâa Allah MaÉaukakin Sarki Ya saka masa da alheri, Ya Ćara masa arziki mai albarka, Ya ba shi lafiya da tsawon rai, tare da Ćara masa ikon ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su amfani alâumma. Muna kuma roĆon Allah Ya sanya wannan kyakkyawan yunĆuri ya zama silar Ćarin ayyukan ci gaba a TumÉurkai da ma sauran yankuna.
Hakika, idan alheri ya fara, kuma aka saurari muradin jamaâa, kammala shi shi ne ginshiĆin nasara. Muna fatan ganin hasken fitilun TumÉurkai ba wai kawai a t**i ba, har ma a zukatan alâummaâhaske na tsaro, haÉin kai da ci gaba.
Allah Ya sanya alheri ya dore. Ameen.
âď¸
Civic-Minded Patriot
Audi Sani