
10/05/2024
Saƙon Juma'a
A cire tatsuniya da shaci-faɗi, a fuskanci zahiri. Duk Fillanin dake duniya babu waɗanda s**a samu wayewa da ɗaukaka da daraja fiye da Fillanin Ƙasar Hausa. In akwai su kuwa, a fito fili a gaya mana.
Kunga ashe duk mai hankali zai fahimci cewa Hausa ce ta sanya wa Fillani rigar da suke taƙama da tinƙaho da fankama da ita. In ba domin Hausa ba, da Fillanin Ƙasar Hausa basu bambanta da danginsu na sauran ƙasashe ba.
Saboda haka in akwai wanda zai yi wa wani gori tsakanin Fillani da Hausawa, to ba Fillani bane zasu yi wa Hausawa gori.
Mu a NIGERIAN BAHAUSHE, bama yiwa kowa gorin Hausa, bama kuma goyon bayan hakan. Mun daɗe da fahimtar cewa ɗaya daga cikin sirrin ɗaukakar ƙasar Hausa da harshen Hausa, shine rungumar baƙi ba tare da nuna wariya ko ƙyama ba.
Saboda haka duk abin da zai je ya dawo ba za mu watsar da wannan halin na karamci da duniya ta san Hausawa da shi ba. Amma ba zamu mance maganar kakanninmu Hausawa ba cewa 'makaho bai san kana kallon sa ba, sai ka zungure shi'.
Muyi Juma'a lafiya.
NIGERIAN BAHAUSHE a san gaskiya da ɓata akan hujja!
© The Nigerian Bahaushe