Funtua News24

Funtua News24 Funtua News24 Domin samun labarun garin Funtua da kewaye a lokacin da suke faruwa.

LABARI DA ƊUMI ƊUMI Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta umarci rufe dukkan makarantun gwamnati d...
21/11/2025

LABARI DA ƊUMI ƊUMI

Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta umarci rufe dukkan makarantun gwamnati da ke faɗin jihar saboda dalilai na tsaro.

Ma’aikatar ta ja hankalin iyaye, malamai da al’umma gaba ɗaya da su bi wannan umarnin nan take, yayin da ake ci gaba da bibiyar yanayin tsaron jihar baki ɗaya don tabbatar da kare rayuwar ɗalibai da ma’aikata kamar yadda majiyar mu Katsina post ta ruwaito.

Ya kuke kallon wannan matakin da gwamnatin Jihar Katsina ta dauka?

Ku bayyana mana ra'ayin ku a kan batun.

DADUMI-DUMI: Soja Yarima yasha dakyar a kokarin hallakashi yanzu cikin daren nan a Abuja, kamar yadda jaridar VANGUARD t...
16/11/2025

DADUMI-DUMI: Soja Yarima yasha dakyar a kokarin hallakashi yanzu cikin daren nan a Abuja, kamar yadda jaridar VANGUARD ta ruwaito.

Rahoton ya nuna cewa Sojan ya lura da wasu mutane da s**a rufe fuskarsu a cikin motoci biyu kirar Hilux dai-dai gidan mai din NIPCO dake Abuja s**a biyoshi, inda ya samu yasha dakyar.

Innalillahi Wa'inna ILaihi Raji'una!Ana sanar da rasuwar Alhaji Sale Ɗanɗa, wanda ya rasu yanzu.Za a gudanar da jana’iza...
15/11/2025

Innalillahi Wa'inna ILaihi Raji'una!

Ana sanar da rasuwar Alhaji Sale Ɗanɗa, wanda ya rasu yanzu.

Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:00pm a yau Asabar, 15/11/2025, a gidansa dake Lungun Aya Primary School, Funtua.

Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa.

DA ƊUMI ƊUMI - Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da fetur da dizalHuku...
13/11/2025

DA ƊUMI ƊUMI - Gwamnatin Tarayya ta dakatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da fetur da dizal

Hukumar kula da harkokin man fetur (Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority – NMDPRA) ta bayyana cewa ba za a aiwatar da kudirin karin harajin kashi 15 cikin dari kan shigo da man fetur (PMS) da dizal ba.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, George Ene-Ita, ya fitar a shafinsu na X (da aka fi sani da Twitter) a ranar Alhamis, inda ya ce aiwatar da harajin da aka tsara baya cikin tsarin gwamnati a halin yanzu.

Hukumar ta tabbatar da cewa akwai wadataccen isasshen man fetur, dizal da iskar gas (LPG) a kasar, wanda ake samu daga masana’antun cikin gida da kuma shigo da su daga waje, domin biyan bukatar al’umma musamman a lokacin bukata ta musamman.

NMDPRA ta bukaci ‘yan kasuwa da masu motoci da su guji boye mai, saye da fargaba ko kuma kara farashi ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa za ta ci gaba da sa ido a kasuwa tare da daukar matakan da s**a dace domin tabbatar da cewa babu tangarda wajen rabon man.

“Hukumar na godewa dukkan masu ruwa da tsaki a sashen man fetur bisa kokarinsu na tabbatar da isar mai ba tare da katsewa ba, kuma muna tabbatar da aniyar mu na kare tsaron makamashi a kasa,” in ji sanarwar.

Ministan Tsaro ya Kare Sojan Ruwa da Yayi Wa Wike MartaniMinistan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa gwamnati za ta...
12/11/2025

Ministan Tsaro ya Kare Sojan Ruwa da Yayi Wa Wike Martani

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana cewa gwamnati za ta kare Laftanar Yerima, jami’in sojan ruwa da ya yi takaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan filin da ake zargin mallakin tsohon hafsan rundunar ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo ne.

Badaru ya ce, “Za mu ci gaba da kare jami’inmu. Ya yi aikinsa yadda ya kamata, kuma ba za mu bari wani abu ya same shi ba.”

Yanzu-Yanzu: Ganduje da Gwamna Abba Gida-Gida sun hadu a Airport.
11/11/2025

Yanzu-Yanzu: Ganduje da Gwamna Abba Gida-Gida sun hadu a Airport.

ALLAHU AKBARHotunan jana’izar babban Limamin Masallacin Juma’a na JIBWIS, dake Funtua, Goni Sheikh Sa’idu Musa Funtua.Al...
10/11/2025

ALLAHU AKBAR

Hotunan jana’izar babban Limamin Masallacin Juma’a na JIBWIS, dake Funtua, Goni Sheikh Sa’idu Musa Funtua.

Allah ya jikansa da rahama!
10/11/2025

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.Allah ya yiwa SHEIK GONI IMAM SA'IDU MUSA a FUNTUA rasuwa, a yau Litinin 10-11-2025Za...
10/11/2025

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN.

Allah ya yiwa SHEIK GONI IMAM SA'IDU MUSA a FUNTUA rasuwa, a yau Litinin 10-11-2025
Za'ayi Zana'idar shi karfe 2pm na rana a kofar gidan shi dake Sabon Layi Funtua.

Allah ya gafarta masa kurakuran sa ya yi masa rahama.

18/10/2025

DA DUMI-DUMI: Anyi zargin shirya yin juyin mulki a Najeriya, Inji Sahara Reporters.

Address

Tudun Malamai
Funtua
830101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua News24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Funtua News24:

Share