
18/11/2024
Hadith of the day
Daga Ɗan Abbas, yardar Allah ta tabbata a gare shi,yace" wata rana nakasance bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gareshi,sai yace"
"Ya kai yaro zan sanar da kai wasu kalmomi:kakiyaye Allah sai ya kiyaye ka,kakiyaye Allah kasamu tsirar sa,idan za kayi roƙo karoƙi Allah,idan zaka nemi taimako kanemi taimakon Allah,
Kasani cewa"Da dai dukkan al'umma zasu taru domin su taimake ka da wani abu,bazasu iya taimakon ka da komai ba face abunda Allah yatsara gareka,
Kuma da ace mutane zasu taru domin su cutar da kai,to bazasu iya cutar da kai da komai ba face abunda Allah yatsara gareka, anɗauke Alƙalumma kuma takardu sun bushe.....
TIRMITHI
Sheikh ja'afar mahmud Adam fans