Ƙarfi ya zo ɗaya tsakanin Zimbabwe da Super Eagles a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.
Yaya kuka ga wasan?
17/11/2023
Kimanin hazikan Yan Wasan Kwallon kafa mutum takwas ne (8) s**a samu nasarar shiga cikin sahun Yan Wasan da aka zaba domin fitar dasu ya zuwa kasa shen SARBIA da Lithuania a Katsina.
Wadannan matasa sun samu wannan nasara ne a gasar baje kolin basirar hazikan Yan Wasan Kwallon kafa da Shugaban Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina United Alh Kabir Dan'lami Rimi hadin gwiwa da Darakta Janar na Dikko Sports Movement Abubakar Sani s**a shirya wato "Katsina Football Scouting program" a Turance
Yan Wasan da s**a samu nasarar sun hada da Yan Wasan Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina United guda biyu sai Kuma sauran Yan Wasan guda Shidda da s**a futo daga kungiyoyin Kwallon kafa daban daban a cikin birnin katsina da kewaye
Su dai wadan Nan Yan wasa da aka dauka zasu samu fita waje ne ta hanyar daukar dawainiyar su da Shugaban Kungiyar Kwallon kafa ta Katsina Alh Kabir Dan'lami Rimi zai yo ta hanyar Yi masu Visa da Kuma Samar masu da dukkannin abubuwan da suke bukata ba tare da sisin kwabon su ba.
16/11/2023
Nigeria league and their gate fees.the most expensive league in Africa 🙄🙄🙄
14/11/2023
An shirya gasar bajakolin neman haziƙan yankwallon Katsina da za'a fidda zuwa ƙasar waje.
A yau ne aka fara gasar bajekolin neman yanwasan ƙwallon ƙafa daga Katsina da za'a fitar zuwa ƙasar waje.
Katsina Post ta samu cewa an shirya gasar mai suna (Katsina Football Scouting program) ƙarƙashin jagorancin shugaban Kungiyar Kwallon ƙafa ta Katsina United Alh Kabir Dan'lami haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar Dikko Sports Movement Abubakar Sani.
A ƙalla kungiyoyin Kwallon kafa goma Sha Shidda ne s**a halarci gasar dake gudana a babban filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium da ke cikin garin Katsina.
Sannan an ɗauko masana wasan Kwallon kafa daga kasa shen Serbia da Kuma Lithuana domin daukar wasu daga cikin su zuwa kungiyoyi daban daban a kasashen ketare.
26/10/2023
*SARKIN YARBAWAN FUNTUA CUP COMPETITION SECOND EDITION*
Be the first to know and let us send you an email when Funtua Football News Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.