
10/04/2025
New World Order (Sabon Tsarin Duniya)
Wanne hali zaka shiga,ko kuma wanne yanayi zaka kasance idan abin da kake bautawa ya bayyana a sararin samaniya ya cika ta fal kuma yana magana da kai da Yaren da kake ji ?
Zaka ji abin kamar shirme ko ? To ina tabbatar maka wannan tsari yayi nisa kuma yana kusa da faruwa ƙarƙashin shirin "Project Blue Beam" da Manyan ƙasashen Duniya da kungiyoyin "illuminati" da da hannun babbar ƙungiyar nan mai kula da duniya da sauran duniyoyi Wato "NASA".
suna shirin amfani da hotunan hologram, sautukan kwakwalwa (ELF), da mu’ujizai na ƙarya domin su jefa duniya cikin tsoro da ruɗani, sannan su kafa tsarin da suke so wanda s**a kira da "New World Order"
Za su yi amfani da waɗancan dabaru kamar haka;
•Kana Zaune ba kowa kusa da kai ƙilama kana kwance a ɗaki zaka ji ana yi maka magana a kunne da sunan wai "Allah" ne ke baka Umarni.
•Kana Tafiya Zaka Iya ɗaga Kai Ka gano Wata Babbar Siffa tana baka Umarni a sararin Samaniya da Nufin Wai Allah ne, kuma da Yaren da kake ji kuma baka kaɗai zaka Ganshi ba ko ku biliyan ne a wajen.
Meye Ƙudurinsu akan haka ?
Ƙudurinsu shine tsarin "New World Order".
Meye "New World Order?
Suna so ne ya zama sune suke juya duniya gaba ɗayanta bisa tsarin
•Addini Ɗaya
Wanda za'a Yaudari Mutane ta Hanyar Fasaha da Wancan Allah na Bogi Mai bayyana a sararin samaniya.
Sannan a ƙirƙiri Annabawan Kowanne addini da muke da shi na Bogi su dinga bayyana a sararin Samaniya ko cikin ɗakun nan mu suna mana magana kai tsaye don ruɗar damu.
•Gwamnati guda ɗaya ce za ta mulki duniya gaba ɗaya.
•Masu kuɗi da Fasaha su ne za su sarrafa dukkan komai na duniya daga abinci zuwa
hankali.
Wadanda ake zargi a cikin wannan ta'asar:
Kungiyoyin Mulhidai na duniya,Kungiyoyin Illuminati, Freemasons, Bilderberg Group
Manyan kasashe kamar USA, da manyan hukumomi irin su UN, World Bank, da IMF duk sune masu wannan Badaƙalar.
Sauran Bayani Duba A Comment Section...