
24/04/2025
Kungiyar Super Tiger ta Funtua ta fara Gasar NLO da kafar dama, inda ta lallasa Bakori FC da ci 2-0 a wasan da aka fafata a filin wasa na Kano.
Wasan ya kasance cike da kuzari da dabaru, amma jarumin matashin dan wasa Adamu, wanda aka fi sani da Vardy, ya zama tauraron rana. Shi ne ya jefa dukkan kwallayen biyu da s**a tabbatar da nasarar Super Tiger a wannan karawa ta farko.
Yanzu tambayar ita ce: Wane mataki kuke fatan kungiyar Super Tiger za ta kai a wannan gasa ta NLO?
Ku ci gaba da kasancewa damu don samun labaran wasanni da dumi-duminsu!