04/12/2025
Ka duba girman darajar da Allah ya ba Annabi Muhammad (SAW), da yadda yake matuƙar sonmu — mu al’ummarsa. Wannan darajar tasa ta shafi mu sosai.
Malam ya bada labari cewa: Wata rana ana zaune, sai Manzon Allah (SAW) ya fito ya ce:
“Ku ji albishirinku! Kuna so ku kasance ku ne kashi ɗaya cikin huɗu na mutanen Aljanna?”
Wato idan an raba duk mutanen Aljanna gida huɗu, al’ummar Annabi Muhammad (SAW) su kasance 25%. Sahabbai s**a yi murna s**a yi kabbara.
Sai Annabi (SAW) ya ce:
“Ko kuna so ku zama kashi ɗaya cikin uku?”
S**a sake yin kabbara da farin ciki.
Daga nan sai Manzon Allah (SAW) ya ce:
“Ina roƙon Allah ku ne ku ɗauki kashi hamsin cikin ɗari na mutanen Aljanna.”
Wato 50% na dukkan mutanen Aljanna — rabin Aljanna gaba ɗaya.
Malam ya ce: Idan mutum ya shiga Aljanna ya leƙa gefe, zai ga mutane biyu — ɗaya daga cikinsu tabbas al’ummar Annabi Muhammad (SAW) ne.
Duk waɗanda Allah ya halitta tun farkon duniya, al’ummomi daban-daban, annabawa da mabiyansu — duk su ne za su raba sauran 50%, yayin da al’ummar Annabi Muhammad (SAW) su ke ɗauke da rabin Aljanna su kaɗai.
Wanda zai fi yawan mabiya bayan Annabi Muhammad (SAW) shi ne Annabi Musa. Wasu annabawa ma ba za su tashi da ko mutum ɗaya ba, wasu biyu ko kaɗan.
Amma saboda girman darajar Annabi Muhammad (SAW), al’ummarsa s**a zama rabin mutanen Aljanna.
Wannan shi ne babban alfarmar Manzon Allah da darajar da muka samu saboda shi.
ALLAH YAKARA MANA SON ANNABI SAW