
01/05/2025
Shugaban Koriya ta Arewa ya ba da
umarnin shirya makamin nukiliya
Kafofin yaɗa labara a Koriya ta Arewa
sun ce Shugaba Kim Jong-un ya umarci
rundunar sojin ruwansa da ta gaggauta
kai makaman nukiliya jiragen ruwa.
Kamfanin dillancin labaran a Koriya ta
Kudu sun ce an bayar da umarnin ne
bayan shugaban Koriya ta Arewa ya sa
ido kan gwajin makaman da ƙasarsa ta
yi na baya-bayan nan.
Masana sun ce akwai yiyuwar a ɗaura
wa jiragen ƙananan makaman nukiliya
masu cin gajeren zango.
Mista Kim ya kuma ƙaddamar da ƙarin
wani katafaren jirgin ruwa da za a iya
amfani da shi wajen harba makamin
na nukiliya.